ANNABI DA SAHABBANSA // 003



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA // 003
.
Qabilar Hamir: Daular Iraniyawa Ta Mulki Qasar Iraqi Da Wasu Yankoki Da Suke Kewaye Da Ita Tun Shekaru 558 Kafin Haihuwar Annabi Isa As, Babu Wani Mahaluki Da Ya Taba Sanya Musu Kara A Gaba Har Zuwa Shekaru 326 Kafin Haihuwar Annani Isa As, Inda Maqduni Ya Far Musu, Ya Karya Qashin Bayansu, Daular Tasu Ta Iraniyanci Ta Tsattsage, Sai Aka Bar Sarakunan Yanki Suka Ci Gaba Da Mulki.
.
A Shekara Ta 230 Ne Kafin Isa As Aka Sami Wasu Yaqoqi Wadan Da A Qarshe Suka Dawo Da Wadannan Yankoki Qarqashin Sarkinsu, Wato Ardashir, Ba Shakka Wannan Sarki Ya Maido Musu Da Qarfin Da Suka Tafka Asararsa, Wasu Daga Cikin Larabawan Dake Zaune A Yankin Suka Yi Hijira Zuwa Sham, Mutanen Hira Da Ambar Kuma Suka Miqa Wuya, Har Ma Da Iraqin, Da Wasu Yankoki Na Jazira Wato Rabi'a Da Mudar.
.
Amma Duk Da Haka Ardashir Ya Fahimci Cewa Mamaye Larabawannan Kai Tsaye Abu Ne Mai Wahala, Sai Ya Qirqiri Samar Da Wani A Cikinsu Wanda Zai Riqa Qarfafashi Ta Nan, A Daya Hannun Kuma Larabawan Za Su Taimake Shi Kan Yaqoqin Da Yake Fama Da Su Tsakaninsa Da Rumawa, Ko Tun Can Rumawan Sun Yi Irin Wannan, Ta Yadda Suka Mamaye Sham, Shi Kuma Ardashir Sai Ya Yi Niyyar Dora Larabawan Iraqi A Kansu, A Taqaice Dai Larabawa Ba Su Sami 'yancinsu A Hannun Iraniyawa Ba Sai Bayan Haihuwar Annabi Saw Da 'yan Watanni.
.
Sarakunan Sham: In Ba A Manta Ba Mun Yi Bayani A Baya Cewa Ba Syria Ce Kadai Ake Kira Sham Ba, Sau Tari In Ka Ji Sham Palestine Ake Nufi, Masamman Inda Ake Batun Fituntunun Banu Isra'ila, Sham Ta Hada Da Syria, Jordan, Lebanon Da Ita Palestine Din, Larabawan Yankokin Iraqi Da Dama Sun Gudu Sabo Da Tsarin Mulkin Iraniyawa Kamar Yadda Muka Fadi A Sama, Suka Dawo Yankin Sham, Inda Suka Hadu Da Sauran Larabawa 'yan Uwansu, Daular Rum Ta Hadasu Qarqashin Masarauta Guda, Da Nufin Su Rinqa Kare Ta Daga Hare-haren Larabawan Qauye, A Gefe Guda Kuma Su Fuskanci Iraniyawa.
.
Kenan Za Mu Fahimci Cewa Larabawa Da Qasashensu Ba A Mamaye Su Don Kwadayin Abubuwan Da Suke Da Shi Ba, Wadannan Qasashen Suna Aiki Da Su Ne Kawai Don Tunkude Matsalolin Da Suke Tsakaninsu, Haka Rum Suka Samar Da Masarautar Gasasana A Dumatul Jandal, Suna Yi Wa Rum Din Biyayya Har Zuwa Lokacin Da Aka Yi Yaqin Yarmuk A Shekara Ta 13 Bayan Hijira, Qarshen Sarkinsu Ya Shiga Muslunci A Lokacin Umar Bn Khattab Ra, Da Wannan Maganarmu Ta Baya Da Muka Ce Ba Su Da Cikakken 'yanci Za Ta Fito.
.
Hijaz:* Su Kuma Yankin Saudiya Kenan A Taqaice, Su Kuma In Za Mu Yi Maganarsu Sai Mun Koma Baya, Yadda Isma'il As, Wato Yaron Ibrahim As Ya Ci Gaba Da Riqe Ragamar Wannan Wuri Na Tsawon Rayuwarsa, A Matsayin Mai Kula Da Daki Mai Alfarma, Sai Dai Kuma Bayan Rasuwarsa Da Lokaci Mai Tsawo Qarfin Jikokinsa Ya Riqa Lalacewa A Hankali, Har Ma Ya Yi Rauni Gaba Daya Dab Da Bayyanar Bukhtanasar, Sai Ya Zama Qabilar Adnan Su Suka Amshe Ragamar, Sai Dai Kuma A Dalilin Yaqin Bukhtanasar Din Adnaniyawan Sun Fantsama Cikin Yaman.
.
A Shekara Ta 687 Kafin Haihuwar Annabi Isa As, Su Kuma Jurhum Suka Takura Wa Mahajjata, Suka Wawushe Kudin Daki Mai Alfarma, Wannan Lamari Ya Dami Adnaniyawa Sosai Ganin Haka Sai Khuza'a Suka Ribaci Halin Da Suke Ciki Suka Far Ma Jurhum Din, Har Takai Ga Ala-tilas Dole Su Bar Yankin, Ganin Haka Sai Suka Toshe Rijiyar Zamzam, Suka Qarqarje Wurin, Suka Rufe Karikitai A Ciki, Suka Qara Gaba Zuwa Yaman Inda Yake Asalinsu, Sun Yi Matuqar Baqin Ciki Da Rabuwa Da Garin Makka.
.
To Sai Dai Bayan Wannan Lamari Khuza'a Su Suka Ci Gaba Da Riqe Makka Har Tsawon Shekaru Dari Uku, A Wannan Lokutan Kuwa Adnaniyawa Sun Watsu A Duniya, Wasu Na Najad, Wasu Kuma Sun Koma Gefen Bahrain Da Iraq, Sai Quraishawa Suka Rage A Cikin Makka Amma Lamarin Kula Da Dakin Allah Ba Shi A Hannunsu, Har Sai Lokacin Da Qusayyi Ya Dawo Cikin Makka Tukun, Inda Yaqi Ya Barke Tsakanin Khuza'a Din Da Quraish, Har Dai Quraishawa Suka Sami Galaba A Kan Khuza'a, A Shekara Ta 440, Sai Quraishawa Suka Sami Damar Mulkar Dakin Allah Mai Girma, Da Jagorancin Qusayyi.
.
Tarihi Ya Nuna Cewa Shi Qusayyin Ya Yi Tsare-tsare Da Dama Ya Kuma Janyo Dansa Abdu-manaf A Jiki, Bayan Rasuwarsa Abdu-manaf Din Ya Ci Gaba Da Kula Da Dakin Allah Da Lamarin Mahajjata Bayan An Tabka Rikici Tsakanin 'yan Uwa Wanda Ya Kusa Aukar Da Yaqi, Shi Ma Abdu Manaf Din Yana 'ya'ya Da Dama, Amma Da Ya Rasu Yaran Suka Yi Quri'a, Sai Kula Da Mabudan Dakin Allah Ta Dawo Hannun Hashim, Bayan Rasuwarsa Dan Uwansa Abdul-muttalib Ya Ci Gaba, To Har Dai Muslunci Ya Zo Jagoranci Yana Hannun Abbas Ne Dan Abdul-muttalib, Su Kuma Suka Raba Lamarin Cikin Wani Tsari Mai Kama Da Damukradiya A Yau, Sai Dai Abin Kula Babu Masarauta Babba Mai Tsarin Fada Ko Tun Farko A Tsakaninsu.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)