ANNABI DA SAHABBANSA // 004



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA // 004
.
Ta Bangaren Siyasa Kuwa, Zahirin Gaskiya Duk Wadannan Masarautun Na Larabawa Da Suke Da Maqwabtaka Da Manyan Daulolinnan Guda Uku Wato Iran, Rum Da Habasha Ba Abin Da Suke Yi Sai Tabarbarewa, Don A Kullum Cikin Wahala Suke, Yau Ka Gan Su Shugabanni, Gobe Talakawa, Duk Kuwa Da 'yancin Da Ake Cewa Suna Da Shi, Ko Suna Mulkar Kansu A Qarshe Dai Qoqarinsu Shi Ne Tara Wa Manyan Daulolincan Jangalin Da Za Su Karba A Lokacin Da Suka Ga Dama.
.
Galibi Akan Karba Ne Da Niyyar Wai Za A Taimaka Musu Ta Fuskar Rayuwa, Ko Za A Tara Makamai Da Dai Sauransu, Kamar Dai Yadda Har Yanzu Iran Take Tatsar Masu Jibantarta Da Sunan Khumusi, Wasu In Ka Ji Su A Sham Yau, Gobe Sai Ka Ji Wadancan A Yaman, Jibi Kuma Wasu Ka Ji Sun Fada Iraq, Duk Da Cewa Ana Yi Musu Qaryar Cewa Masarautunsu Nasu Ne, Amma A Zahiri Ma'aikata Ne Kawai Na Wadancan Daulolin.
.
Su Kuwa Hijaz Da Ba Su Da Maqwabtaka Da Wadancan Daulolin Gaskiya Ko Sauran Larabawan Suna Girmamasu, Suna Yi Musu Kallon Jagorori Masamman Yadda Yankin Ya Zama Cibiyar Addini, Matsayinsu Na Kula Da Daki Mai Alfarma, Da Kula Da Baqi Wajen Ba Su Masauki Da Ciyarwa Ya Sa Dole Suka Qirqiri Wani Qwaryaqwaryar Shugabanci, Kuma Ko Tun Da Can Suna Kan Addinin Annabi Ibrahim Ne As Da Ya Bar Wa Isma'il As.
.
Sun Bambanta Kenan Da Daular Rum Da Habasha Da Suka Riqi Kiristanci, Ko Iran Da Ta Riqi Majusanci (Wato Bautar Wuta) A Matsayin Ibada, Duk Da Cewa Mutanen Makka Da Kewaye Sun Tsara Wannan Shugabanci Da Muka Ce Masa Qwarya-qwarya, Sai Dai Bai Da Wani Tasirin Da Zai Iya Kare Kansa, Shi Ya Sa Ma Da Abrahata Ya Ce Zai Rushe Dakin Da Shugabancinsu Ya Damfaru A Kai Ba Wani Abin Da Suka Iya Yi, Sai Cewa Kawai Suka Yi: "Mai Shi Zai Kare Abinsa, Wato Allah Sw, Kuma Tabbas Ya Tsare Dakin, Za Mu Yi Bayani Dannan Gaba.
.
A Addinance Kuwa Larabawan Hijaz Sun Iya Tsare Kansu Wajen Bin Addinin Annabi Ibrahim As, Tun Lokacin Da Suka Amsa Kiransa, Sai Dai Rayuwar Yau Da Kullum Ta Sa Sun Yi Rauni Har Sun Zubar Da Manya-manyan Abubuwa Sai Wadan Da Ba Za A Rasa Ba, Wannan Ya Sa Qaramin Abu Ma Yana Iya Batar Da Su, Da Sannu Har Jagoran Khuza'a Wato Amr Bn Luhai Ya Dulmiyar Da Su.
.
Tabbas Zai Iya Yin Hakan Don Ya Taso Ne Cikin Kyawawan Dabi'u, Ga Sadaqa Ga Qoqarin Kare Addini Daidai Gwargwado, Da Haka Sai Jama'a Suka So Shi Sosan Gaske, Har Suka Sanya Shi Cikin Manyan Malamai Da Waliyai, To Da Ya Je Qasar Sham Ne Ya Ga Yadda Yadda Suke Bautar Gumaka Sai Abin Ya Ba Shi Sha'awa Har Ya Yi Zaton Abu Ne Na Haqiqa, Domin Sham Ne Cibiyar Manzanni Da Littafan Da Aka Riqa Saukarwa.
.
Lokacin Da Zai Dawo Sai Ya Zo Wa Makkawa Da Hubal Aka Sanya Shi A Qa'aba, Daganan Ya Kira Su Zuwa Yin Shirka Da Allah, Amsa Masa Da Suka Yi Sai Sauran Hijaz Suka Bi Su Domin Makkawa Ne Shugabanni Ta Fuskar Addini, Ita Kuwa Manata Tana Can Ne Gabar Tekun Maliya Kusa Da Qadid, Su Kuma 'yan Ta'if Suka Dauki Lata, A Wadin-nakhla Kuma Suka Sanya Uzza A Gaba, Wadannan Su Ne Manya-manyan Gumakan Da Suke Ji Da Su, Daga Kansu Ne Gumaka Suka Qaru Har Suka Mamaye Hijaz, Shirka Ta Zagaye Ko'ina.
.
Wannan Ya Sa Fitaccen Addinin Larabawa A Jahiliyya Ya Zama Bautar Gumaka, Tare Da Raya Cewa Suna Addinin Ibrahim Ne As, Mafi Yawancin Bukuwan Shirkar Da Suke Yi Amr Bn Luhai Ya Kawo Musu, Su A Ganinsu Bidi'a Ce Amma Mai Kyau, Kamar Dai Yadda Yanzu Kowa Ya Sha Iska Sai Ya Ware Jama'a Ya Yi Ta Azabtar Da Su, Yadda Suke Yi Kuwa:-
.
1) Sukan Gurfana Wa Gumakan Ne, Su Riqa Daga Murya Suna Neman Mafaka A Wurinsu, Suna Fado Buqatunsu Tare Da Sa Ran Samun Biyan Buqata.

2) Sukan Niqi Gari Daga Wuri Daban-daban Don Jewa Yi Musu Dawafi Tare Da Qanqan Da Kai._

3) Sukan Yi Ta Zuwa Da Dabbobi Suna Yanke-yanke A Gaban Gumakansu Tare Ambato Buqatansu.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)