ANNABI DA SAHABBANSA// 005



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA// 005
.
Duk Da Cewa Bayanan Da Muke Yi Yanzu Kan Addinin Larabawa Ne, Mazauninsu Da Mutanensu, Zai Yi Kyau Kuma Mu Duba Wadan Da Ba Larabawan Ba Kuma Suka Iya Canja Addinin Na Larabawan Wato Addinin Annabi Ibrahim As Zuwa Nasu, Misalin:-

A. SABA'ANCI:* Wani Addini Ne Na Maguzanci, Da Ya Yi Tasiri A Yaman Da Yankunan Iraqi, Ya Hadu Da Yahudaci Lokacin Zuwansa, Ya Sake Cakuduwa Da Nasaranci, Ramukan Bautarsu Da Kufayensu Har Yau Dinnan Akan Gani A Yankunan Iraqi Da Sham.
B. YAHUDAWA: Su Ne Wadan Da Bukhtanasar Ya Yaqe Su A Shekara Ta 587 Kafin Haihuwar Annabi Isa As, Ya Kama Wasu Da Dama, A Wannan Dalilin Sai Wasu Kaso Mai Girma Ya Gudo Zuwa Hijaz Inda Larabawa Suke, Misali Madina Da Sauran Wurare, Suka Samu Suka Yi Kaka-gida Har Suka Fara Samun Mutane A Hankali.
.
Amma Babban Hijirar Yahudawa Zuwa Madina Ta Samo Asali Ne A Shekara Ta 70 Miladiya, Lokacin Da Rumawa Suka Mamaye Palestine, Suka Takura Wa Yahudawan Sosai, Ya Sa Dole Suka Bar Nan Suka Koma Madina, Khaibar Da Taima, Suka Qirqiri Wasu 'yan Qauyuka, Wasu Wuraren Kuma Suka Zauna A Wasu Tsaunuka, Da Wannan Addininsu Ya Dan Fara Bazuwa Har Wasu Larabawan Suka Yi Sha'awa Suka Karba, Wannan Ya Sa Har Suka Iya Yin Tasiri A Lokacin Shugowar Addinin Muslunci.
.
Shugowar Muslinci Ya Zo Ya Sami Qabilun Yahudawa Kusan Ashirin Da Wani Abu A Cikin Larabawa, Sai Dai Biyar Ne Suka Yi Fice, Wato: Khaibar, Nadeer, Mustalaq, Quraiza Da Qainuqa, Za Mu Iya Cewa Yahudanci Ya Shiga Yaman Tun Zamanin As'ad Bn Karb Ne, Inda Ya Je Yaqi Madina A Qarshe Ya Koma Da Yahudanci Tare Da Wasu Malaman Yahudawan Guda Biyu Daga Banu Quraiza, Daganan Yahudanci Ya Fara Yaduwa A Yankin, To Da Dansa Yusuf Zunawas Ya Hau Ne Ya Sa Aka Riqa Haqa Rami Ana Jefa Kiristocin Najran Da Rai Kamar Yadda Muka Fadi A Baya.
.
C. KIRISTANCI: Kiristanci Ya Sami Shiga Qasashen Larabawa Ne Ta Hanyar Mamayar Da Daulolin Rum Da Habasha Suka Yi Wa Yaman, Don Habasha Sun Mamaye Yaman Tun 340 Miladiyya, Wanda Ya Kai 378, A Wannan Lokacin Ne Kiristanci Ya Ratsa Cikin Larabawa, Da Yake Muslunci Bai Je Can Ba Addinin Allah Dai Sai Shi, Lokacin Ne Wani Zahidi Mai Tsoron Allah Da Ake Amsar Addu'arsa, Kuma Yake Dauke Da Wasu Karamomi Sunansa Fimyon Ya Isa Can, Yayin Da Ya Ga Alamar Gaskiya A Tare Da Su Ya Kira Su Ga Addininsa Kuma Suka Amsa.
.
To Har Dai Kisar Gillar Da Aka Yi Musu Qarqashin La'anannen Jagoranci Na Yahudanci, Nan Ne Suka Yi Rauni, Amma Dawowar Da Habasha Ta Yi Don Taimaka Musu Qarqashin Nasarancin Ta Taimaki Abrahata Wajen Yada Kiristancin A Ko'ina Cikin Yankin, Har Ma Yake Ganin Ba Addinin Da Za A Yi Sai Nasarancin, Shi Ne Ya Yi Qoqarin Rushe Qa'aba, A Qarshe Allah Sw Ya Gama Da Shi, Shi Da Mabiyansa, Wadan Da Suka Karbi Addinin Ciki Har Da Larabawan Gasasana, Tai Da Taglib Sabo Da Rum, Da Yaman Sabo Da Habasha.
.
D. MAJUSANCI: Mafi Yawan Larabawa Sun Auka Majusanci Ne Ko Bautar Wuta Sabo Da Maqotakarsu Da Qasar Iran, Kamar Dai Iraq Da Ihsa Wanda Yake Bahrain, Da Sauran Qasashen Dake Gabar Tekun Larabawa Kamar Yaman, Har Ma Su Yaman Din Suka Sunkuya Musu Lokacin Da Iran Din Ta Mamaye Su, Har Yanzu Kuma Suna Qoqarin Maida Su Gidan Jiya Qarqashin Majusancinsu Amma Wannan Karon Da Sunan Shi'a, A Zahiri In Yaman, Syria Da Iraq Sun Koma Shi'a Ba Wani Mamakin Da Za A Yi In Dai Za A Kalli Tarihi Da Tasirantuwarsu Da Addinai Daban-daban.
.
To Haka Dai Muslunci Ya Zo Ya Sami Larabawa Da Wadannan Addinai Daban-daban, Wadan Da Suke Cewa Suna Addinin Ibrahim As Tabbas Sun Bar Shi, Sun Yi Nisa Da Barin Koyarwarsa Sun Dauki Wani Abu Daban, Kamar Dai Gumaka, Suka Bar Allah Suka Riqe Su, Yahudawa Kuma Suka Debi Wani Kaso Suka Mai Da Su Bayi, Suka Yi Ta Hada Rikici, Suna Sayar Da Makamai Suna Tara Kudi Da Mamaye Wuri, Kiristoci Kuma Abin Ya Rikice Wa Mabiyan, Yadda Suka Kasa Bambance Mahalicci Da Abin Halitta, Shi Ya Sa Masu Addini Cikin Larabawan Ba Su Damu Da Addinin Ba, Sauran Addinan Kuma Su Da Mushirikan Duk Daya Ne Ba Wani Bambanci.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)