*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //015❤️💞*
*(C) Baban-Manar Alqasim*
Dangane da wahayin da ya riqa sauko wa Annabi SAW kuwa, matarsa A'ishah RA take cewa: "Farkon abin da aka fara yi wa Annabi SAW wahayi da shi shi ne tabbataccen mafarki, bai yin wani mafarki sai ya zo masa kamar wulqawar walqiya, sai kuma aka sanya masa son kadaituwa, ya riqa kadaita a kogon hira yana bauta, na tsawon wasu kwanaki sai daga baya ya koma gida ya sake sabon shiri, sannan ya je wajen Khadijah RA ta ba shi kwatankwacin wanda ya samo, har dai tabbatan lamari ya same shi a kogon, mala'ika ya same shi ya ce " Karanta"
.
Na ce "Ni fa ba na karatu" ya kama ni ya qaqume ni sai da na wahala sannan ya sake ni ya ce "Karanta" na ce masa "Ba na karatu" ya sake kama ni ya qaqume ni, a karo na uku ya ce ={Karanta da sunan Ubangijinka da ya yi halitta• Ya halicci mutum daga gudan jini• Karanta lallai Ubangijinka shi ne mafi karamci}= haka manzon Allah SAW ya koma da su zuciyarsa tana bugawa.
.
Ya shiga wurin Khadijah RA yana cewa "Lullube ni! Lullube ni!! Har sai da kaduwar ta rabu da shi sannan yake cewa Khadijah RA " Me ya faru ne?" Daga bisani ya kwashe labari ya gaya mata, ya ce "Har na ji wa kaina tsoro" Khadijah RA ta ce "Ina! Allah ba zai tabar da kai ba, kana sada zumunta, kakan dauki nauyin wasu, ka kawo abin da aka rasa, ka girmama baqo, ka yi taimako a lokacin masifu" daga nan ta tafi da shi wurin baffanta Warqatu bn Naufal bn Asad bn Abdil Uzzah.
.
Shi wannan Waraqan a lokacin da Quraishawa suka kama bautar gumaka sai shi ya zama Nasara, har ma yana rubutun Injila da yarensu na Ibiranci, duk da cewa ya girma matuqa, ta ce "Dan uwana saurari abin da danka yake cewa" Warqa ya ce "Dana me kake gani?" Annabi SAW ya gaya masa komai, sai Warqa ya ce "Wannan mala'ikan da ya je wa Musa ne, ina ma a ce ina da rai ina da qarfina lokacin da mutanenka za su kore ka!"
.
Sai manzon Allah SAW ya ce " Za su kore ni?" Ya ce "Qwarai kuwa, ai ba a taba samun wanda ya zo da irin abin da ka zo da shi ba sai an yi gaba da shi, in dai wannan lokacin ya same ni zan yi matuqar taimakonka" daganan bai jima ba ya rasu)To bayan saukar wahayin ne ya sami kansa cikin wani yanayi na damuwa da firgici, har na tsawon wasu kwanaki, wannan sabo da ganin abin da bai saba gani ba ne, da tsoron yadda zai kasance a gaba.
.
Tarihi ya yi bayanin yadda damuwar take kai shi har qololuwar manyan duwatsu, don ya goce wa abin da yake ganin shi ne zai faru da shi, sai dai duk yadda ya hau dutsen Jibril AS zai fito masa ya ce "Muhammad SAW tabbas kai manzon Allah SW ne" sai hankalinsa ya kwanta ya sami natsuwa, daganan sai ya dawo gida, in ya sake jimawa sai wancan yanayi ya sake dawo masa, malamai sun yi ta bayani kan yadda aka sami hikimar daukewar wahayin, don Annabi SAW ya sami natsuwa ne daga wancan firgicin.
.
Arrazi RL, yake cewa a cikin tafsirinsa 31/192 an sami sabani kan tsawon lokacin da wahayin ya yanke, Ibn Juraij ya ce kwana 12 ne, Alkalbi ya ce kwana 15, Ibn Abbas ya ce kwana 25, Suddiy da Muqatil suka ce kwana 40, almuhim in muka lura gaba-daya dai wasu 'yan kwanaki ne ba wai yanayin ya ci gaba ne har zuwa qarshen rayuwarsa ba, kuma lokacin da ya sami natsuwa, ya tabbatar da cewa lallai fa yanzu shi Annabi Allah ne, mai bullo masa dinnan kuma mai kawo masa wahayi ne daga Allah SW sai ya sami natsuwa daganan sai Jibril AS ya dawo masa.
.
A cikin Buhari 2/733 Annabi SAW yana cewa: "Ina cikin tafiya sai na ji wani sauti daga sama, na daga kai, sai ga mala'ikan da ya zo min a kogon Hira, yana zaune a kan kujera tsakanin sama da qasa, sai na razana har na yi qasa, na dawo wajen iyalina na ce " Ku rufeni! Ku rufe ni!! Ku rufe ni!!!, sai Allah SW ya saukar da Muddatthir wato ={ Kai wanda aka lullube }= har zuwa inda ya ce Fahjur, daganan ne kuma wahayin ya ci gaba da bibiyan juna, wato ya ci gaba da sauka akai-akai.
Zamuci Gaba Inshaa Allaah...
*Gabatarwa: Zauren Sunnah*
*WhatsApp @Zauren Sunnah*
+2348039103800.
