ANNABI DA SAHABBANSA //016



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //016❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

Irin wannan hali da Annabi SAW ya shiga kafin bibiyar wahayi ya tabbatar da dan adamtakarsa kasancewar shi mutum ne kamar kowa ta wurin halitta, sai annabta da manzanci suka raba shi da sauran mutane, a tarihance mun san mahaifiyarsa da ma abubuwan da suka faru tun kafin haihuwarsa, da rasuwar iyayensa da kakanni, mun kuma yi bayanin dabi'unsa, saura kuma mu san yadda sifarsa take, a wajen bincike mun yi qoqarin tsayawa a kan ingantattun hadisai kawai.
.
Da farko dai Annabi SAW a sifance kyakkyawa ne yadda za a iya fadin kyawunsa, idan muka duba Buhari 3549 da Muslim 2337 za mu ga inda Barra yake cewa (Ya fi kowa kyawun fuska da kyawun halitta SAW) wato a halitta ma Allah SW ya kyautata surarsa. 
.
Sannan shi ba dogo ne cancan ba yadda in mutum ya zo fadin yadda yake ya sifanta shi da tsawo, sannan kuma ba gajere ne yadda za a kamanta shi da gajarta ba, kenan yana tsaka tsaki, an samu a Buhari 3549 da Muslim 2337, inda Barraa yake cewa " Shi ba dogo ne ba cancan ba kuma gajere ba" a Buhari 3547 Anas RA yana cewa: Matsakaici yake tsakanin mutane, ba dogo can ba ba kuma gajere ba.
.
Ta wajen launin fata kuwa, SAW fari ne, amma ba cancan da zai nuna shi daban ba, wato a yi tsammanin zabiya ne a tsakaninsu, ba kuma fari ne mai duhu-duhu ba, Anas bn Malik a hadisin Buhari 3547 Muslim 2330 yake cewa: Fari ne shi ba na illa ba, ba kuma mai sirkin duhu ba.
.
A yanayin hasken fusa da tsarin sa kuwa yana da fadin fuska kamar yadda muke cewa rounded face, ta yadda Jabir bn Sumra RA yake cewa: Wani mutum ne ya yi tambaya, ya ce "Fuskarsa kamar takobi ce?" Sai ya ce "A'a, kamar rana ce da wata, zagayayya" ka duba Muslim 2344.
.
Simak bn Harb yana cewa game da yadda bakin Annabi SAW yake, ya nuna ba tsukakke ba ne, sannan tsagin idanunsa dogo ne da sifa mai kyau, ya ce: Na ji Jabir bn Sumra RA yana cewa: Ba mai qaramin baki ba ne kuma mai dogon tsagin idanu ne Muslim 2339.
.
Gashin kan Annabi SAW da na bi hadisan na fahimci ruwayoyin gwargwadon yanayin da kowani rawi ya ga Annabi SAW ne a lokacin, Anas bn Malik RA ya ce: "Gashin Annabi SAW ba saukakke ne har kafada ba, ba kuma tattararre ne mai quda-quda ba, ya bar shi tsakanin kunnensa ne da wuyarsa" Buhari 5905, Muslim 2338, a wani hadisi na Anas din dai ya ce: " Gashinsa ya riqa tabar kafadunsa" Buhari 5903, Muslim 2338.
.
Bayan duga-dugansa kuma bai ciko yadda zai yi muni ba, Jabir bn Sumra yake cewa a hadisin da Muslim ya rawaito 2339: "Bai da tarin nama a bayan duga-dugansa".
.
Dangane da taushin hannunsa kuwa, Anas bn Malik yake cewa: " Ban taba taben wani qyallen siliki ko alhariri wanda ya fi hannan Annabi SAW taushi ba, Muslim 2330.
.
Sai Abu Juhaifa ya ce: Na kama hannun Annabi SAW na dora a kan fuskata sai na ji ya fi qanqara sanyi, ya kuma fi almiski qamshi,Buhari 3553.
.
In ba wannan ba to sai dai tambarinsa na annabci dake bayan kafadunsa, masamman ta bangaren hagu-hagu, ya dan fito ya yi kamar tarin nama, yana da qananan suma a kansa, mun riqa fadin girmansa, ko na ce ana cewa ya fi qwan tantabara bai kai dunqular hannu ba.
.
Bayanai kala daban-daban mutum zai iya karantawa a kan sifofin Annabi SAW, na kadaita da wadannan ne don komawa kan batun da muke yi na tarihin Annabi SAW da sahabbansa, sannan mu dan goce wa wasu abubuwan da ba mu da tabbaci a ciki.
.
Wannan aiki da aka dora wa Annabi SAW na kawo saqo zuwa ga jama'arsa babban aiki ne da za mu iya raba shi zuwa gida biyu:-
a) Garin Makka: inda ya kusan kwashe shekaru goma sha uku ya na kiran mutane zuwa ga Allah.
.
Madina: Nan kam dududu shekara goma ya samu, in an hada su duka biyu sun zama 23, ga 40 kafin annabci sun zama 63, na Makka din ma za a iya kasa shi zuwa gida 3, shekara 3 ya kwashe yana kiran mutane a boye, sai kuma bayyanar da'awa a farkon shekara ta 4 bayan annabci, har zuwa ta 10, sai kuma da'awa a wajen Makka daga shekara ta 10 din har hijira zuwa Madina.

Zamuci Ga
Post a Comment (0)