ANNABI DA SAHABBANSA // 018



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

   ANNABI DA SAHABBANSA // 018
.
_Duk Da Cewar Kiran Da Ake Yi Wa Mutane Zuwa Muslunci A Boye Ake Yi, Amma Labari Ya Kurdada Har Zuwa Kunnen Quraishawa, Sai Dai Ba Su Damu Da Sha'aninsa Sosai Ba, Ko Don An Yi Wasu Irinsa Masu Magana Kan Kadaita Allah Ne Oho, Don An Yi Umayyata Bn Abi Salt, Qussu Bn Sa'ida Da Amr Bn Naufal, Akwai Ma Wasu Ban Da Su, Sai Quraishawan Suka Zaci Shi Ma Annabi Saw Nan Zai Yi Ya Qare Irinsu, Amma Da Suka Ji Qarfinsa, Da Yadda Labarinsa Ya Fara Bazuwa Ko'ina, Sai Suka Fara Sanya Masa Ido._
.
_A Dan Wannan Lokaci Dake Buqatar Sirri Musulmai Duk Suka Zama 'yan Uwa Masu Taimakon Juna, Kowa Kuma Ya Fara Tunanin Yadda Zai Jawo Wani Kusa Da Shi Kamar Dai Yadda Abubakar Ra Ya Yi, Har Yawansu Ya Dan Qaru, A Qarshe Allah Sw Ya Ba Da Damar Bayyana Da'awar A Sarari._
.
                  ```BAYYANA DA'AWA```
_Koda Yake An Yi Umurni Da Bayyana Da'awar Amma Ba Cewa Aka Yi Ga Kowa Ba, Allah Ya Umurci Annabi Saw Ne Da Ya Janyo 'yan Uwansa Na Kusa Tukun A Suratus Shu'ara 214, Farkon Abin Da Annabi Saw Ya Yi Shi Ne Ya Kira Danginsa Na Kusa Banu Hashim, Da Wasu Kadan Daga Cikin Banu Abdilmuttalib, Adadinsu A Lokacin Ya Kai 45, Nan Take Abulahab Ya Ce "Wadannan Dai Baffanninka Ne Da 'ya'yansu, Don Haka Yi Magana Kai Tsaye Ba Wasa Ba._
.
_"Ina So Ka Sani, Danginka Ba Su Iya Komai Da Daukacin Larabawa, Ni Ya Fi Dacewa Na Dakatar Da Kai, Ka Tsaya A Dangin Babanka Kawai, Don In Za Ka Ci Gaba Da Abin Da Kake Yi Ya Fi Musu Sauqi Da A Ce Quraishawa Gaba-dayansu Sun Taru Maka, Sauran Larabawan Ma Su Taya Su, Ni Ban Taba Ganin Wanda Ya Jajubo Wa Danginsa Bala'i Irinka Ba" Sai Annabi Saw Ya Yi Shuru, A Ranar Dai Ba A Iya Gudanar Da Komai A Taron Ba, To Amma Fa Annabi Saw Neman Wani Lokaci Yake Yi Da Ya Fi Wannan Dacewa, Haka Dai Ya Sake Tara Su A Karo Na Biyu._
.
_Ya Miqe Ya Yi Addu'ar Da Ya Saba Yi Sannan Ya Ce "Jagora Dai Ba Ya Wa Mabiyansa Qarya, To Na Rantse Da Wanda Ba Wani Abin Bautawa Da Ya Cancanta Sai Shi, Ni Manzon Allah Ne Gare Ku, Kuma Da Sauran Jama'a Gaba-daya, Na Rantse Da Allah Za Ku Mutu Kamar Yadda Kuke Barci, Kuma Za A Tashe Ku Kamar Yadda Kuke Farkawa, Sannan Za A Yi Muku Hisabin Ayyukanku, Ko Dai Ku Tabbata A Wuta Ko A Aljanna" Abutalib Ya Nuna Suna Son Taimaka Masa, Kuma Sun Karbi Nasiharsa, Sun Gasgata Maganarsa._
.
_Ya Ce "Wadannan Danginka Ne, Ni Ma Daga Cikinsu Nake, Sai Dai Na Fi Su Saurin Isa Inda Kake So, Ci Gaba Da Abin Da Aka Sanya Ka, Wallahi Har Yanzu Ina Tare Da Kai Kuma Zan Kare Ka, Duk Da Cewa Raina Yana Liqe Da Addinin Abdulmuttalib"._
.
_Abulahab Ya Ce: "Wallahi Wannan Aika-aika Ce, Gwara Ku Hana Shi Kafin Wasu Su Riga Ku" Abutalib Ya Ce "Mu Kuwa Wallahi Za Mu Tsaya Masa Matuqar Muna Da Rai" Lokacin Da Annabi Saw Ya Tabbatar Da Cewa Abutalib Ya Yi Alkawarin Ba Shi Kariya A Yayin Da Zai Isar Da Saqon Ubangijinsa Sai Wata Rana Ya Miqe A Kan Dutsen Safa._
.
_Ya Daga Murya Duk Quraishawa Suka Taru Don Jin Abin Da Zai Ce, Sai Ya Kira Su Zuwa Ga Kadaita Allah Sw, Da Yin Imani Da Saqonsa Da Ranar Lahira, Kamar Dai Yadda Ya Zo A Buhari Cewa Wanda Bai Iya Fitowa Ba Ma Ya Sa A Jiwo Masa, Abulahab Ya Zo Cikin Quraishawa, Annabi Saw Ya Ce "In Na Gaya Muku Cewa Mahara Na Gefen Gari Suna Son Auka Muku Za Ku Gasgata Ni?" Suka Ce "Ba Ka Taba Yi Mana Qarya Ba" Ya Ce "To Ina Yi Muku Gargadin Azaba Mai Radada" Abulahabi Ya Ce "Kai Tir! Da Ma Don Wannan Ka Tara Mu?" Sai Tabbat Ta Sauka._
.
_Akwai Wani Hadisi Wanda Muslim Ya Rawaito Na Abu-huraira Yana Bayanin Wancan Taron, Ya Ce: "Lokacin Da Ayar ={Ka Gargadi 'yan Uwanka Makusanta}= Ta Sauko, Sai Annabi Saw Ya Kira Su, Ya Yi Wa'azi Ga Daukacin Jama'a Gaba Daya, Ya Kuma Kebe Na Kusa, Sai Ya Ce " Quraishawa Ku Kubutar Da Kanku Daga Qunar Wuta, Banu Ka'ab Ku Kubutar Da Kanku Daga Qunar Wuta, Fatima 'yar Muhammad Saw Ki Kubutar Da Kanki Daga Qunar Wuta, Na Rantse Da Allah Sw Ba Ni Da Wani Abin Da Zan Iya Yi Muku A Wurin Allah, Sai Dai Akwai Zumunci Tsakanina Da Ku, Kuma Zan Sada Shi._

_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)