*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*💝💞TSAKANIN SO DA SOYAYYA //34💝💞*
*(C) Baban-Manar Alqasim*
To kai maigida ga mu mun dawo kanka, mai yuwuwa kai ke dandana kudarka a cikin gida, sau da yawa ba ka samun abin da kake so, sabo da dalilai masu dama, daga cikinsu har da abin da nake so mu fahimta a yau, haqiqa rayuwar aure ba abu ce da take da iyaka ba, haqiqa ma ba a fatar a ce an sanya mata lokaci, wannan shi ne bambancinta da zina, ko kuma auren holewa, wanda ake cewa aure ne amma na wasu 'yan sa'o'i ko kuwa a debi wasu 'yan kwanaki ana holewa da 'ya'yan jama'a, in kudinka sun qare kowa ya kama gabansa kamar yadda Daduro yake, sai dai abin da zai baqanta rai shi ne a dauki wannan holewar a matsayin addini, wace aka kira ta zina ba mai yi sai jahilai da marasa tsoron Allah.
Auren holewa in dai aka ce addini ne to ba shakka malamansu ne za su fi kowa yi sabo da tunanin sun fi kowa tsoron Allah, a hakan kuma suna da kamammun matansu a gida ba mai taba su sai su kadai, to ka san kana da auren addini, dole ka tsare gidanka, in an sami baraka ma da hannunka, aka ce 'in bera na da sata to daddawa ma tana wari' laifukammu wajen zabo matan aure Allah kadai ya san iyakansu, da yawammu mukan auri mata ne don soyayya kawai, don ta burge mu ko don tana da kaza da kaza.
In dai ran mutum yana son mace shi kenan, ko ta rasa qima ta addini ba matsala ba ce, tana da tarbiyya ko ba ta da shi duka daya ne, wani ma ko matar ba ta qaunarsa zai aura, don jikinta kawai yake buqata kamar dai 'yar zina da 'yar holewa bai damu da musayar qauna ba don bai shirya wa hakan ba, dole dai mu sake nazari; Wa za mu aura? Ko ya rayuwar za ta kasance bayan aure? Duk auren da za a yi cikin murna da farin ciki amma nan da nan ya juye ya zama ba mai natsuwa da juna to barinsa shi ya fi.
Wani ya kan fara neman mace, har ta qare ta fito sarari ta nuna masa cewa ba ta fa qaunarsa, amma mannirun ya dage sai ya aura, in ka yi masa magana ko ka ba shi shawarar ya haqura, nan fa zai dage ya ce "Ai za ta bari yaranta ce kawai" ko ma ya ce " Kunya ce, ka san budurwa" ita kuwa hankalinta sam-sam ba ya tare da shi, irin wannan in aka nace sai auren ya zama na dole, tabbas zai taki shimfidarsa yadda yake so, amma fa zuciyarta ba ta tare da shi.
Akwai mata birjik suna auren mazan da ba sa qaunar su, mazan sun kasa dasa soyayya a qirazansu, tsakaninsu da matansu kawai shimfida, a irin wannan yanayin ne sai in matan suka ga dama sai su riqa motsa kishin mazan, wajen yin hira da tsofaffin samarinsu, kodai a waya kai tsaye ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani, wanda yin hakan shi yake bata wa mata addini kuma ya yi sanadiyyar asarar aljannarsu ba tare da ta sani ba, matar aure tana ma'amalla da maza.
Kai a matsayinka na maigida kana buqatar mace mai tausayi, wace za ta qaunace ka tsakaninta da Allah? Ka sani, duk macen da ta iya ba ka zuciyarta, tabbas za ta iya yin komai sabo da kai, don ta san rayuwarta tana hannunka ne, Aljannarta ma za ta samu ne a sakamakon tsoron Allanta da kuma yanayin biyayyar da ta yi maka, Allah ya fadi a Qur'ani cewa bai halicci aljani da mutum ba sai don su bauta masa.
Ya kuma fadi cewa ayarsa ce da ya halitta wa maza mata don su sami natsuwa a wurinsu, ashe yana daga cikin hikimar halittar mace don ta yi wa mijinta hidima, ta qaunace shi ta tausaya masa, shi kadai kawai ba tare da motsa kishinsa ba, mace kenan ta qwarai ba ballagaza ba wace kowa zai bi ta kanta ya wuce arha, in kana buqatar mace ta gari wace aka halicce ta don kai daya kal, wace ba ta damu da mazan fesbuk ko wotsap ba, wani shiri ka yi don haka?
In dai ka auro 'yar holewa komai baqin hijabinta ka san abin da zai faru, ko da kuwa ba ka da kishi, don raba wa maza kanta ba wai haramun ba ce addini ne ma a wajenta, kuma ta riga ta saba, sannan ba wai 'yar holewa ce kadai ba, na sha ganin soyayya mai tsananin gaske tsakanin talaka da 'yar mai kudi, ko tsakanin talaka da mai kudi, wani yakan kai ga gaci, wani kuwa tir da alatsine su ne kan gaba.