ANNABI DA SAHABBANSA //035



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //035❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*AMBASADAN MUSLUNCI NA FARKO A MADINA*
To da yake mubaya'ar a lokacin aikin hajinsu ne, suna gamawa sai ya hadu su da ambasadon farko a Yathrib don ya koyar da su abubuwan da suka shafi musluncin, ya kuma fahimfar da su addininsu, ya taimaka wajen yada muslunci ga wadan da haskensa bai riga ya kai gare su ba, don haka ya zabi wani matashi majiyi qarfi wato Mus'ab bn Umair Al'abdariy RA, lokacin da Mus'ab RA ya isa can sai ya sauka a gidan As'ad bn Zurara, da shi cikin wadan da Annabi SAW ya fara magana da su, da kuma wadan da suka yi masa muba'aya.
Wadannan mutane guda biyu RA, suka ci gaba da yada muslunci a Yathrib, wani abin ban sha'awa da aka hakaito kan wadancan samarin RA: Wata rana As'ad RA ya dauki Mus'ab RA suka nufi gidan Banu Ashhal da Banu Zafar, sai suka shiga daya daga cikin gonakin Banu Zafar, suka zauna a bakin wata rijiya ana ce mata Maraq, har wasu daidakun musulmai suka same su a can, to Sa'ad bn Mu'az da Usaid bn Hadeer a sannan ba su muslunta ba, suke shugabantar qabilarsu ta Banu Ashhal.
Da suka ji abin dake faruwa sai Sa'ad ya ce da Usaid "Je ka ka ja wa wadancan mutanen kunne, sun zo ne su yaudari masu rauni a cikimmu, ka ce musu kar su qara zuwa gidammu, don ma As'ad bn Zurara dan innata ne wallahi da na yi maganinsu!" Usaid na isowa sai As'ad ya ce wa Mus'ab RA, "Wannan da kake gani shugaban jama'arsa ne, nemi taimakon Allah kawai a kansa" Mus'ab ya ce "In dai zai zauna, ni kuwa zan shawo kansa" 
Usaid ya qaraso a murtuke ya tsaya a kansu yana cewa "Me ya kawo ku wurimmu? Wato kun zo ne ku yaudari raunanammu ko? To in dai kuna da buqatar rayukanku, lallai hawainirku ta kiyayi ramarmu" Mus'ab ya ce "Ko kuma dai kai ka dan zauna ka ji abin da ya kawo mu, in ya yi maka ka amsa, in bai yi ba ka dauki mataki kan abin da ba ka so ka ji" sai ya ce "I wannan kuma gaskiya ne!" Ya caka mashinsa a qasa ya zauna, Mus'ab ya yi masa fashin baqi game da muslunci, ya karanta masa Qur'ani, sai ya ce "Wallahi mun ga hasken muslunci a fuskarsa tun bai furta ba, can sai ya ce " Wannan abu da ban sha'awa, to ya ake yi in za a shiga wannan addinin?"
Sai suka ce masa "Kawai ka yi wanka ka tsarkake tufafinka, sai ka yi kalmar shahada ka yi nafila raka'a 2" bayan ya yi abin da aka zayyano masa sai ya ce "Akwai wani can na baro shi a baya, in da za a yi dace ya bi ku, to da ba wanda zai saba masa a cikin jama'arsa, bari na je na janyo muku shi" ya finciko mashinsa ya kama hanya, shi kuma Sa'ad na hango shi yana zuwa dandalinsu sai ya ce "Wallahi ba da fuskar da ya je ya dawo ba" Usaid na qarasowa Sa'ad ya ce "Uhm?" Usaid ya amsa masa "Na yi musu magana, amma wallahi ban ga wani abin zargi tare da su ba, da na hana su sai suka ce ka yi abin da ka ga dama.
Ya ci gaba da cewa " To dama na ji cewa Banu Harithah sun san As'ad bn Zurara dan innarka ne, to sun kintsa kashe shi, qila shi ya sa ya zo buya a nan!" Jin haka sai qabilancinsu ya motsa, ya fisgi mashinsa ya nufe su, sai dai kuma da ya iske su bai ga wata alama ta tashin hankali tare da su ba, nan ne ya hararo cewa tabbas Usaid tunkudo shi ya yi don ya saurare su, shi ma ya tsaya tserere ga mashi a hannu, sai As'ad ya ce masa "Abu Umamah, wallahi ba don zumincin dake tsakanina da kai ba da ba mu zo nan ba, mun gwammace abin da zai same mu ya same mu a gidajemmu.
Mus'ab ya gaya wa Sa'ad irin abin da ya gaya wa Usaid har ya zauna, shi ma suka yi kamar dai yadda aka yi da Usaid, ya muslunta ya koma ya sami mutanensa ya ce " Banu Abdil'ashhal wace iriyar sheda za ku yi min?" Suka ce "Kai shugabammu ne, kuma mafi hangen nesammu" sai ya ce "To daga yau na haramta wa kaina magana daku, mazanku da matanku har sai kun yi imani da Allah da manzonsa, sai duk suka yi imani in ba mutum guda rak ba.
Shi wannan bawan Allan da bai muslunta ba sunansa Usairim, Allah cikin ikonsa ba shi ya muslunta ba sai ranar yaqin Uhudu, ranar ya muslunta, kuma ya yi
Post a Comment (0)