ANNABI DA SAHABBANSA // 06



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA // 06
.
Jahiliyya Kalma Ce Da Ta Shahara A Bakin Masu Rubuta Tarihi, Har Wasu Masu Karatunsa Suka Zaci Larabawa Jahilai Ne A Lokacin, A Zahiri Ba Jahilci Ba Ne Gidadanci Ne, Kuma Duk Wata Al'ummar Da Za Ta Ajiye Addini Ta Dauko Wani Abu Ta Saka A Matsayin Addinin Dole Ta Fuskanci Irin Wannan Matsalar, Koda Yake Kowa Ya Sani Ba Su Iya Rubutu Da Karatu Ba, Amma Duk Wani Mai Ilimi Ya Sani Cewa, Wannan Zamani Ya Qare Tun Lokacin Da Aka Aiko Annabi Saw A Matsayin Manzo, Sannan Kuwa Babu Zancen Rubutun Da Qaratu, Amma Gidadancin Ya Qare.
.
Sannan Ba Duka Larabawan Ne Ake Yi Musu Kudin Goro Ba, Dabi'unsu Sun Bambanta Da Juna, Kowani Mutum A Cikin 'yan Uwansa Mai Daraja Ne, Kowa Yana Iya Ba Da Jininsa A Kansa, To Bare Mace, Wace Matsayinta Mai Matuqar Girma Ne A Wajen Mijinta, Kuma Zai Iya Ba Ta Kariya Ko Ta Halinqaqa, Ba Wani Namijin Da Zai Kusance Ta, Wasu Ma Sukan Rasa Rayukansu A Kan Mace, Koda Kuwa Ba Matar Aure Ce Gare Su Ba.
.
Kenan Ba Su Yi Kama Da Dabbobi Ba Yadda Kowani Namiji Zai Iya Zuwa Wurinta Da Sunan Aro, Wannan A Jahiliyya Ma Kenan, Shi Ya Sa In Jarimi Zai Yi Kirari Sai Ka Ji Mace Ya Fara Ambatowa, Kai Abin Ya Kai Ga In Mace Tana Son Ta Hada Kan Qabilun Da Suke Yaqi Da Juna Za Ta Iya, In Ma Gwara Kansu Take So Ta Yi Cikin Sauqi Za Ta Aikata, Duk Da Cewa Har Da Haka Namiji Yana La'akari Da Kansa A Matsayin Jagora Kuma Mai Ba Da Kariya Ga Iyalin, Tare Da Cewa Dole Maganarsa Ce Za A Dauka A Matsayin Umurni.
.
Da Yake Muslunci Bai Bayyana Ba A Lokacin, Sukan Yi Aure Kala-kala Wasu Tabbaci Suna Da Ban Dariya A Wannan Zamani Da Muke Ciki:-

1) Akwai Irin Auren Da Ake Yi Yanzu, Wanda Mutum Zai Je Gidan Uban Yarinya Neman Aurenta, Ya Kuma Ba Da Sadaqi A Qarshe Ya Aure Ta Cikin Mutunci.

2) Akwai Kuma Wanda In Mutum Yana Son Dansa Ya Zama Jarimi, Sai Idan Matarsa Ta Gama Al'ada Ya Riqa Turata Gidan Wani Jarumi, To Ba Zai Kwanta Da Ita Ba Har Sai Cikin Jarumin Ya Bayyana Sannan Ta Tsaya Wa Maigidanta.
.
3) Akan Sami Mutanen Da Ba Su Kai Goma Ba Su Yi Ta Za Ga Mace Guda, Har Sai Ta Dauki Ciki, To Bayan Ta Haihu Sai Ta Tura Musu Gayyatar Cewa Ta Haihu Su Zo, Ba Wanda Ya Isa Ya Noqe, A Nan Ne Za Ta Zabi Wanda Take So, Sai A Jingina Masa Dan A Ce Nasa Ne.

4) Wadannan Kam Tamkar Karuwai Ne, Yadda Mace Za Ta Daga Tuta, Duk Mai Sha'awa Sai Ya Je Ya Biya Buqatarsa, In Ta Sami Ciki Sai A Kira Masu Ilimin Damgane Don Su Zo Su Fidda Uban Yaron, Shi Kuma Bai Da Ikon Da Zai Yi Jayayya Ya Ce Ba Dansa Ba Ne.
.
A Haka Ne Allah Sw Ya Turo Manzonsa Ya Narka Dukkan Aurarrakin Da Aka Yi A Baya Ya Tabbatar Da Qwara Daya Wato Muslunci, Wani Auren Mutu'a Da 'yan Shi'a Suke Yi Yau, Ko Aron Farji Qari Ne Daga Wadan Can Aika-aikar Na Zamanin Jahiliyya, Don Akan Hada Gasar Yaqi A Kan Mace, Wanda Ya Yi Nasara Ya Dauke Matan Dayan Gaba Dayansu, Sukan Auri Mata Kuma Ba Adadi, Ba Kamar Yadda Ake Auren Mata 4 Yau Ba.
.
Batun Wadancan Aurarrakin A Ce Sun Yi Kama Da Zina Gaskiya Ba Ma Zancen Yi Ba Ne, Don Zina-zinace A Lokacin Kala Daban-daban Bai Da Haddi Ko Adadi, Sai Dai 'yan Daidaiku Na Qwarai Wadan Da Ba A Rasawa, Don Abin Ya Kai Ga Cewa Ba A Cika Damuwa Ba Don An Ce Wane Dan Zina Ne, Abin Takaici Kawai A Ciki Shi Ne Muguwar Qaunar Da Ake Yi Wa Mace, Tare Da Qyamar Samun 'ya Mace Ta Kowani Hali.
.
Don Wasu Daga Cikinsu Sabo Da Ganin Yadda Ake Barna Da 'ya'ya Mata Sai Suka Yanke Kawai Su Riqa Rufe Yaran Kawai, Abin Dariya Ko Na Ce Abin Tausayi Shi Ne Imanin Mutum Ba Zai Bar Shi Ya Kashe 'yarsa Da Hannunsa Ba, Gwara Kawai Ya Rufe Ta Haka Albashi Dai Bai Ga Yadda Za Ta Qarisa Ba, Shi Ya Sa Wani Zai Turbede Ta Yana Kuka, Duk Da Haka Suna Mugun Buqatar 'ya'ya Maza Don Su Taimaka Musu Wurin Yaqi, Hasali Ma Tsarin Zamantakewar Iyali An Gina Shi A Kan Qabilanci, Ba Ruwansu Da Cewa Nasu Ne Ke Da Gaskiya A Cikin Rikici Ko Shi Ne Azzalumi, Shi Ya Sa Aka Sami Yawan Yaqe-yaqe A Tsakaninsu, Kamar Da Rikicin Aus Da Khazraj, Ko Abs Da Zubyan, Ko Kuma Bakr Da Taglib.
.
To Sai Dai In Ka Sami Qabilolinsu Za Ka Taras Babu Wata Alaqa Ta A Zo A Gani Mai Qarfin Gaske, Kai Dai Bar Su In An Taba Nasu Duk Za Su Yi Hobbasa, Kuma In Dai Watanni Masu Alfarma Suka Zo Akan Dakatar Da Duk Wani Yaqi A Tsakaninsu, Shi Ya Sa Suke Qaunar Watannin Kuma Suke Girmama Su, A Taqaice Dai Duk Wani Gidadanci Da Ka Sani Ana Yi Sun Yi, Shi Ya Sa Fitowar Annabi Saw Ta Zama Rahama Gare Su, Ta Wanke Musu Duk Abin Da Yake Damunsu.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)