TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA AURE
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?
*AMSA*👇
Wa'alaikum salam, In har an San tanada ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi bayan wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.
Auran dá aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba zá'à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.
In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi S.A.W "Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" kamarc yadda Abu-dawud ya rawaito.
In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí dá aka daura.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOKyy👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177