HUDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN ANNABI (S.A.W) DAKE MADINA



HUDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN ANNABI (S.A.W) DAKE MADINA

MAI TAKEN:
LADUBBAN ADO ('KAWA) A MUSULUNCI

*DAGA BAKIN* : 
*ASH-SHEIKH ABDUL-BARI BN AWWAD ATH-THUBAITI*

*WACCE TA FASSARA SHI ZUWA HARSHEN HAUSA* : 
( *OUM HANAN* )

         {{ *SHAFI NA FARKO* }}

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da Iyalansa da sahabbansa da wadanda suka jibince su..

Bayan Haka:
Allah ya 'kawata duniya ya halittata ya kyautata ta, da abubuwan da zasu sakance a cikinta, kuma ya kiyayeta ya sanya kyawu da siffofi masu kyawu a cikinta; Allah Madaukaki Yace:
{Wanda Ya kyautata komai, Wanda Ya halitta shi}.

Allah ya 'kawata sama sannan ya sanya rana, da wata, da taurari su zama ado da 'kawa gareta; Allah Madaukaki Yace:
{Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo} kuma ya 'kawata kasa da duwatsu da bishiyoyi da 'koramu da furanni; Allah Madaukaki Yace a cikin siffantata:
{Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki}.

Kuma ya sanya dabbobin ni'ima su zama kwalliya da ado ga kasa; 
Allah Madaukaki Yace:
{Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba}.

Kuma mafi kyawun abubuwan da Allah ya samarwa mutum ya 'kawata shi da kyawun halitta da kyawun sura, da madaidaiciyar siffa, Allah ya 'kawata shi a cikin halittarsa, kuma ya 'kawata shi a cikin siffarshi; Allah Madaukaki Yace:
{Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka*A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta}.

Ado 'kawa Jin dadi ne da ni'ima, kuma an halicci dan Adam da sonsa; Allah Madaukaki Yace: 
{An Æ™awata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da É—iya da dÅ©kiyõyi abÅ©buwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dÅ©niya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take} 
kuma anan ne girma da darajan addini yake kara daukaka wanda yake karbar abin da mutum yake bukata, kuma ya amsa kiran abin da aka halicci dan Adam akanshi, yayin da Allah ya halattawa bayinSa jin dadi da abin da aka halatta musu, na daga 'kawa wadanda Allah ya fitar dasu saboda bayinsa; Allah Madaukaki Yace:
 {Ka ce: "Wãne ne ya haramta Æ™awar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "SÅ©, dõmin waÉ—anda suka yi Ä©mani suke a cikin rãyuwar dÅ©niya, suna keÉ“antattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani}.

Kuma Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi misali ne daga cikin misalai gurin dai-daituwa gurin yin ado, ya sakance mafi tsaftan mutane kuma mafi tsarkinsu.
Kuma daga cikin shiriyarshi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi akwai yawaita kanmshi (sanya turare)ya kasance baya mayar da turare, kuma yana jin dadin kamshin turare kuma yana cewa:
((Wanda aka bijiro masa da raihan (tsiro ne mai dadin kamshi da sanyi da ake yin turare da shi) to kada ya mayar dashi, domin lallai shi tsiron raihan bashi da nauyi gurin dauka sannan yana da dadin kamshi))
[Muslim ya ruwaito shi].
Post a Comment (0)