KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA- JUGOL- BIU- BORNO STATE
🌐 04/AL-MUHARRAM/1443-HJRY
🌐 13/AUGUST/2021MLDY
🎙️ *GABATARWA👉🏼 Abubakar BN Mustafa Biu*
⭕ *TOPIC👉🏼 {HIKIMOMIN JUJJUYAWAR SHEKARU🌐}*
➖ *mun kasashi gida 4️⃣*
1️⃣➖ *MUQADDIMA*
Yau juma'an farko na sabon shekarar Musulunci *1443-HJR* hakan na nuna an naɗe tsohon shafinmu ɗaukeda kyawawan ayyukanmu cikin *ILLIYAI* da munananta cikin *SIJJINAI* kuma an buɗe mana sabon shafi don ganin me zamu aikata aciki, Haƙiƙa mun ƙetare kwarinda ramukanta tacinye wasunmu basu iya fitowa daga cikintaba, yanzu kuma gamu akan gaɓan wani kwarin saidai kash bamu saniba zamu ƙetara ko kuma zamu faɗa cikinta yadda miliyoyi ko biliyoyi suka faɗa a baya,
2️⃣➖ *YAUSHENE AKA FARA IRGEN KWANAN WATAR MUSULUNCI⁉️*
Zamanin *AMIRUL MUMININ UMAR IBN KHAƊƊAB R/A* shekara ta *16* ko *17* da hijira ya tara mutane don shawartarsu daga ina za'a fara gina irgen kwanan watar Musulunci⁉️◾Wasu sukace= a gina irgen akan haihuwar ANNABI SAW, ◾Wasunsu sukace= a gina irgen da ranarda aka bawa *ANNABI SW* Annabta, ◾Wasunsu kuma sukace= a gina akan ranarda *ANNABI SAW* yarasu,◾Wasu kuma sukace= a gina akan ranarda *ANNABI SAW* yayi hijira,
Ƙarshe dai *UMAR R/A* yarinjayarda afara ginata akan hijira, domin itace shekararda acikinta aka tada komaɗar Musulunci mai cin gashin kanta, kuma acikinta aka samarda farkon garinda Musulmai ke da tacewa akanta *(MADINA)* sai akayi ittifaƙi akan ginawa akan *HIJIRAR*
Sa'annan kuma a wannan taron sukayi shawarar akan wane wata zasu fara ginawa,◾Sai wasu sukace= *RAMADAN* don shine watar sauƙar *QUR'ANI*, saidai *UMAR da UTHMAN da ALIY R/A* sun rinjayarda farawa akan watan *MUHARRAM* domin ita watane mai alfarma, kuma yana biyeda watar *ZULHIJJAH* wanda aciki mutane suka sauƙe hajjinsu🕋 wanda shi hajjin shine cikamakin rukunnan Musulunci, kuma shi hajji shine ƙarshen abinda aka farlanta a rukunan Musulunci guda 5, Sa'annan shi *MUHARRAM* yana bin watanda *ANSARAI* sukayiwa *ANNABI SAW* mubaya'a akan yayo hijira zuwa garinsu, wannan shine Muƙaddimar hijira, sai yazanto shi *ALMUHARRAM* shine mafi dacewar wata dazai zanto farkon shekara,
3️⃣➖ *HIKIMAR JUJJUYAWAR KWANAKI*
Jujjuyawar shekaru da watanni, dare da yini, akwai isassun hikimomi,
Daga ciki ALLAH yasanyata *taskace ga ayyukan alhairi ko sharri* kuma *marhalace ta rayuwar mutane* har zuwa ƙarewar ajalinsu,
Daga hikimarsa- cikin rahamarsa yasanya dare ayarta ƙwallon watane☪️ kuma yasanya mata duhu don sauƙin barci, ya sanya yini kuma ayarta ƙwallon rana ne🔆 kuma yahaskakata domin sauƙin neman abinci, kuma da ita mutum ke sabunta rayuwarsa da ƙarfinsa da fuskantar ayyukansa, domin an anbaci barcin dare da mutuwa, farkawa kuma da tashiwa bayan mutuwa,
💡 *ALLAH SW yace* *<<* kuma shine yake kasheku da dare kuma yasan abinda kuka girba da rana sa'annan yana tayar daku da rana domin irga ajali anbatacce, sa'annan agareshi makomarku yake sa'annsan yabaku labarin abinda kuka aikata *>>*
Cikin hikimarsa da rahamarsa ya sanya rana 🔆 da wata☪️ kayan lissafi, da ƙwallon rana🔆 ake gane lissafin yanayi, da ƙwallon wata☪️ ake gane lissafin watanni, kuma yasanya watannin su *12* ne, wajibine mugodewa *ALLAH SW* don sauƙaƙa mana lissafi don gane wa'adin alƙawura da bashi,
💡 *ALLAH SW yace* *<<* lalle adadin watanni a wurin ALLAH watanni 12 ne a littafin ALLAH tun ranarda yahalicci sammai da ƙassai kuma acikinta akwai 4 masu alfarma *>>*
4️⃣➖ *RUFEWA*
Bayin *ALLAH* gamu nan munga hudowar farkon wannan sabuwar shekarata *1443-HJRY* bamu saniba shin zamuga ƙarshenta ko bazamu ganiba, nawa sukaga farkonnata amma a kwanakinnan huɗun nawa suka mutu? iyaye da uwaye, yara da mata, matasa da tsoffi, mumafa muna nan tafe,
Kada mu manta wannan wata na *MUHARRAM* shine wata na 3 cikin watanni masu alfarma dasuke jere guda 3, kuma muna cikin gomanta nafarko masu falala, tana ƙunshe da ranakun azumtar *TASU'A* da *ASHURA* ana yinsu ranakun *9* da *10* wanda na shekarannan zasu kama ranakun *Laraba* da *Alhamis* masu zuwa,
💡 *ANNABI SAW* yace *"* azumin Ashura tana kankare zunubban shekararda yagabata *"* *[MSLM daga ABU QTD AL-ANSWARY]* don haka mu azumceta mu da iyalanmu,
👏🏻 *ALLAH YASA MUYI RAYUWA LAFIYA KUMA MU WANYE LAFIYA👏🏻*
*AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻*
*via👉🏼Abubakar BN Mustafa Biu✍️*