HUKUNCI KASUWANCI TA INTERNET “ONLINE BUSINESS



HUKUNCI KASUWANCI TA INTERNET “ONLINE BUSINESS”

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

TAMBAYA:
---------------
Mutum ne yake bibiyar kamfanoni, da shaguna da suke tallata kayansu ta hanyar Internet, yanda suke yi kuwa shi ne: sukan sanya hotunan hajar da suke da ita a shafinsu, su kuma bayyana farashin kowanne daga ciki, sannan su bayar da adireshinsu, gami da lambobin waya da za a iya tuntuɓarsu. Sai wannan mutumi da yake bibiyarsu ya kwafi hotunan, ya sanya su a shafinsa, ya tallata wa jama’an da suke bibiyarsa a shafinsa, bayan ya sanya ribarsa a kai, da zaran mutum ya ga hoton abin da yake so, yakan tuntuɓi wanda ya sanya hoton, su yi ciniki, sai ya tura masa da kuɗin ta asusunsa na banki “Bank account”, shi kuma sai ya cire kuɗin, ya tafi, ko ya tuntuɓi masu shagunan, ko kamfunan na asali, ya saya daga wurinsu, ya tura masu kuɗi, su kuma su turo masa da hajar, sai shi kuma ya tura wa waɗanda suka saya daga wurinsa.. Mene ne hukuncin irin wannan kasuwanci a Shari’ar Musulunci?.
-----------------
AMSA:
---------------
BismilLah, walhamdulilLah.. wassalatu wassalamu ala RasulilLah. Wa ala Alihi wa Sahbihi waman walah..
Bayan haka: Allah Maɗaukakin Sarki ya shar’anta hukunce – hukuncen da suke da jiɓi da kuɗi, gami da dukiya da ma sauransu ne, saboda samar wa da ɗaukacin bil’adama da maslaha, da kuma biyan buƙatunsu na yau da kullum cikin wani yanayi na aminci, da zai gadar da zaman lafiya mai ɗorewa, Saboda haka ne Allah Maɗaukakin Sarki ya ba su umurnin aikata wasu abubuwa, ya kuma hana su aikata wasu; domin a tabbatar da adalci ga ɗaukacin ɓangarorin mu’amala, da kuma hana faruwar rikici da saɓanin da zai kai zuwa ga tashin hankali, da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Kawar da rikici gami da saɓani abu ne da yake cikin manyan manufofin Shari’ar Musulunci, a dalilin haka ne ma Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake cewa: (Ba za ku taɓa shiga aljanna ba har sai kun so juna), babu shakka ana son juna ne idan an karya lagon rikici, da saɓani a tsakanin mutane, musamman a wajen mu’amalolinsu na yau da kullum.
Malaman Hadisi da dama sun ruwaito Hadisi daga Sayyiduna Hakim Bn Hizam (Allah ya ƙara yarda da shi) cewa: ya ce: Ya Manzon Allah, mutum ne yakan zo wuri na yana son ya sayi hajar da ni ba ni da ita, shin na amshi kuɗinsa in sayo masa daga cikin kasuwa? Sai ya ce: (Kada ka sayar da abin da ba ka da shi).
Wannan Hadisi yana hana duk wani ciniki akan hajar da mai sayarwar bai mallake shi ya shiga ƙarƙashin ikonsa ba, abin da zai ƙara ƙarfafa wannan ma’anar shi ne Hadisin da Imam Ahmad ya kawo a cikin “al-Musnad” shi ma daga Sayyiduna Hakim Bn Hizam (Allah ya ƙara yarda da shi), ya ce: (Na ce : Ya Manzon Allah, Lallai nakan sayi kayan sayarwa, mene ne ya halatta a gare ni, mene kuma bai halatta a gare ni ba?, Sai ya ce: (Idan ka sayi kaya, kada ka sayar da shi har sai ya zo hannunka), a wani Hadisin Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Duk wanda ya sayi abinci, kada ya sayar da shi har sai ya zo hannunsa), Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas (Allah ya ƙara yarda da su) yana ganin wannan hanin bai taƙaita da abinci kawai ba, a’a ya game komai da komai, inda yake cewa: “Ina ganin komai ma daidai yake da abinci”.
Sai dai duk da haka, ganin cewa Shari’ar Musulunci ta zo ne domin biyan buƙatun bayi, da kuma kawar masu da kowane irin rikici, da tashin hankali, haka ya sanya aka sami sauƙi a wasu daga cikin mu’amaloli na yau da kullum da suke gudana a tsakanin mutane, ko domin al’adarsu ta tafi akan haka, ko kuma sun zamo ruwan dare a cikin al’umma, kuma babu zalunci, da ɓarna a mafi yawan irin waɗannan ma’amalolin, a irin wannan yanayi sai a Shari’a ta halatta irin wannan ma’amala, a wani manhaji da ake kiransa a ilmance da: “ala khilafil asal”, wato saɓanin asali, ko “ala khilafil ƙiyas”, wato saɓanin ƙiyasi, ko “ala khilafi ƙa’ida”, wato saɓanin ƙa’ida, ko kuma a ce: wannan togaciya ce daga ƙa’ida kaza, a cikin ire- iren waɗannan mu’amaloli akwai waɗanda akwai ruɗu “al-Gharar” a ciki, amma shari’a ta halatta su; saboda tsananin buƙatar da ake yi zuwa ga haka, kaman: “Bai’us Salam”, da “Bai’ul Istisna’”.
MA’ANAR “BAI’US SALAM”:
Malaman Fiƙhu sun bai wa “Bai’us Salam” ma’ana da cewa: shi ne kasuwanci a cikin sifan abu da yake kan mai sayarwa, ma’ana, shi ne kasuwancin da mai sayarwa bai mallaki haja a ƙarƙashin ikonsa ba, kawai dai ya bijiro da sifofin hajarsa ne, kuma ya ɗauki alhakin bayar da shi zuwa wani lokaci.. kaman mutumin da yake da gonar da ba ta riga ta gama fitar da amfaninta ba, ko kuma ba su kai munzalin da za a cire su ba, sai dai shi mai gonar ba shi da kuɗin da zai kammala hidimar gonarsa har ta kai zuwa ga nuna, bai kuma sami wanda zai ba shi bashi don ya kammala nomarsa ba, a dalilin haka, yake matuƙar buƙatar hanyar da zai sami kuɗin da zai ƙarisa nomarsa, in kuwa ba haka ba, zai yi asarar wannan shuka da ya riga ya yi, saboda haka ne aka halatta masa yin mu’amala ta hanyar “bai’us Salam”, wato an bashi daman ya sayar da amfanin gonarsa ga wanda zai ba shi kuɗi a nan take -duk kuwa da cewa bai riga ya agama kammala ba tukunnna-, shi kuma ya kammala nomarsa da kuɗin da ya basa, in sun nuna sai ya miƙa amfanin ga wanda suka yi wannan kasuwanci da shi. Lallai buƙata ce ta sanya aka halatta wannan kasuwanci, in ba haka ai shi ma na’u’i ɗaya ne daga cikin nau’o’in sayar da abin da ba a riga an mallaka ba..

DALILAN HALACCI:
Wannan mu’amala ta kasuwanci ta samo asali ne daga maganar Allah mai girma da buwaya da yake cewa: ((Ya ku waɗanda kuka yi imani, idan za ku bayar da bãshi a tsakankaninku zuwa wani lokaci, ya kamata lokacin ya zama sananne, ku rubuta bãshin; saboda kiyaye haƙƙoƙi da gudun rikici)) [al- Baƙra: 282], Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas (Allah ya ƙara yarda da su) ya ce: “wannan ayar ta sauka ne akan sha’anin “Bai’us Salam”.
Haka akwai Hadisi da Imam al-Bukhari, da Imam Muslim suka ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas (Allah ya ƙara yarda da su) cewa: Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya zo Madina ya sami mutane suna yin bashin amfanin gona zuwa shekaru biyu- biyu, da uku - uku, sai ya ce: (Wanda zai bayar da bashin wani abu, to ya bayar a cikin sanannen sikeli, da sanannen ma’auni, zuwa kuma sanannen lokaci), wannan yana nuna halaccin irin wannan kasuwanci, wato “Bai’us Salam”.
A haka kuma aka ƙulla Ijma’in malamai akan halaccinsa. Jamhur ɗin malamai sun tafi akan cewa: an halatta irin wannan kasuwanci “Bai’us Salam” ne; saboda buƙata, domin bai yi daidai da ƙiyasinsa akan “kasuwanci da abin da ba a riga an mallaka ba”, zai dai zamo an sauƙaƙa shi ne kaman yanda aka sauƙaƙa cin mushe, da shan giya a halaye na lalura da taƙura.

MA’ANAR “BAI’UL ISTISNA’”:
Malamai sun bai wa wannan mu’amalar mai suna: “Bai’ul Istisna’” ma’anar cewa: shi ne sayar da wani abu da yake akan mai sayarwa, da sharaɗin zai yi aikin sana’anta shi zuwa wani lokaci, koda dai Malikawa suna ganin cewa ba shi da wani bambanci da “Bai’us Salam” da bayaninsa ya gabata a taƙaice.
Yanda yake kuwa shi ne: Mutum ne zai nemi kafinta ya ƙera masa ƙofa, ya faɗi surar da yake so, su yi ciniki, ya ciro kuɗi ya biya, akan zai ƙera masa ƙofa akan sharaɗin da suka yi zuwa wani lokaci da suka haɗu akansa.
Lallai babu wani saɓani akan halaccin irin wannan kasuwanci, duk da shi ma dai buƙata ce ta sanya aka halatta, domin a asali wannan kasuwanci ba shi da bambanci da sayar da hajar da ba a riga an mallaka a hannu ba, halaccin ya zo ne saɓanin ƙiyasi, kaman yanda malamai suka bayyana.
Lura da bayanan da suka gabata za mu iya cewa: Harkar kasuwanci da ake yi ta Internet (da surar da aka bayyana a wannan tambaya) ta zamowa halatta; sakamakon tsananin buƙatar da ake yi zuwa gare ta, da kuma ganin cewa tana samar da maslaha ga mai saye, da mai sayarwar a tare, sannan kuma yaɗuwar irin wannan kasuwanci tsakanin al’umma, tana nuna cewa: gaskiya da riƙon amana su ne suka fi rinjaye a cikinsa, akan zalunci da cin amana, da suke haifar da rikici da faɗa a tsakanin mutane, bari mu kawo wasu daga cikin fa’idojin irin wannan kasuwanci a taƙaice:
* Kusanto da nesa: da yawa masu sayen kayan ba su da ikon isa zuwa ga kamfuna, ko shagunan na asali; sakamakon nisar da take tsakani, wasu ma daga ƙasashen ƙetare suke.
* Ƙarancin cuta da zalunci: a halin da ake cikin irin wannan kasuwanci ya karaɗe duniya, kuma sifar gaskiya da riƙon amana su suka fi rinjaye a ciki.
* Biyan buƙatar mai saye, da na mai sayarwa: mai saye yana son kayan da ba shi da ikon isa zuwa ga hajar, amma albarkacin wannan kasuwanci ya isa zuwa ga abin nemansa. Shi ma mai sayarwa ya sami riba sakamakon “data” da kuma kai komonsa tsakanin masu haja da mai saye, da ma kuma: ((Allah Maɗaukakin Sarki sauƙi yake so maku, ba ya son ku da wahala..)) [al-Baƙra: 185], mun dai riga mun san cewa: babban manufar Shari’ar Musulunci na sanya dokoki a fagen mu’amaloli na kuɗi shi ne: biyan buƙatun bayi, da kuma hana faruwar rikici, da saɓani da suke kai wa zuwa ga rashin zaman lafiya da tashin hankali..
Allah shi ne masani.
Saleh Kaura
Post a Comment (0)