HUKUNCIN HADA SALLAH ALOKACINDA AKE RUWAN SAMA



HUKUNCIN HADA SALLAH ALOKACINDA AKE RUWAN SAMA

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum
A lokacinda ake ruwan sama ko duhu ana hada sallah to muma mata zamu iya hadawa a gida?

*AMSA*👇

Walaikum sallam
Toh ai bawai mujarradin ruwan saman ko duhun bane yasa ake hada sallah A'a mushaqqace wato idan akace mutane su sake fitowa su dawo masallaci akaro na biyu zasu takura shine yasa ake hada sallah. Shiyasama ake hada sallar azahar da la'asar ai saboda in akayi ruwa lokacin azahar duk gari zezama a jike asamu ta6o da ca6al6ali wanda hakan zesa mutane su takura yayinda zasu dawo sallar la'asar se akace su hada sallah. Toh amma wanda yake sallah acikin gida banajin akwai wata takura akanshi tunda dai agidansa yake bazece acikin gadan nashi ruwan ze biyoshi ya jikashiba kokuma ta6on yabiyoshi har cikin gida ya wahalar dashi kokuma duhun. Kaga kenan illarda tasa ake hada sallah toh shi me sallah agida wannan illar shi bata shafeshiba sam sam. Inkuma yanaso shima ya hada toh seya fito shima yazo masallacin ya hada tareda masu haÉ—awa domin dama saboda anason jam'in shiyasa akace ahada ai jam'inne ba,aso ya su6ucewa mutane kuma babu wanda yace mata basa zuwa masallaci dan haka wacce takeso ta haÉ—a itama seta fito tazo masallacin amma ko namiji wanda zeyi sallah acikin gida toh shima be halasta ya hada ba bare kuma mace wanda dama asali su akasani sukeyin sallah acikin gida.

Allah Yasa mudace

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)