HUKUNCIN WANKAN TSARKI DA SABULU
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum barka da safiya malan inada tambaya kamarhaka nine nikeso nayi waikan. Juma'a kuma inaso nayi waika da sabulu to yaya waikan zankasance ne malan na gode Allah ya sakada mafificin alkairi malan Allah yayi jagoranci
:
*AMSA*👇
:
Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu
Alhamdu-lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad ﷺ.
Musulmin da yayi wakan juma'a sannan yayi wakan sabulu, wankansa ya yi, kuma babu laifi yayi Sallah kai tsayi, idan yayi alwala kuma bai shafi azzakarinsa ba lokacin wankan sabulun. Shafan zakari da cikin tafin hannu yana warware alwala. Domin haka, sai maza su kiyaye. Idan sun shafi al-aura, to sai sun sake alwala.
Babu laifi mutum yayi wankan tsarki bayan yayi wakan sabulu, kamar yadda zai iya yin wankan tsarki sannan yayi wakan sabulu. Wakan tsarki ana yinsa ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato ruwan da dandanonsa bai canza ba, launinsa bai canza ba kuma kamshinsa bai canza ba.
Idan mai wanka zai fara wankan ibada kafin na sabulu, to babu wani khaufi dangane da ruwansa, saidai yakiyaye kar yashafi azzakarinsa bayan alwala. Amma idan mai wanka zai fara na sabulu ne, to ya kiyaye ruwansa kar ya gurɓata da kumfar sabulu har ya canza launinsa, ko kamshinsa, ko dandanonsa.
Allah ya tsare-mana ibadar mu kuma ya karba mana. Amin.
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
