HUKUNCIN YIN WANKA DA DADDARE



HUKUNCIN YIN WANKA DA DADDARE :

TAMBAYA TA 2848
****************
Assalamu alaikum warahmatallah. Malam Allah ya saka da alkhairi yajikan iyayan dangane da irin taimakonka ga al'umma. Ameen
Malam don Allah ka amsa mana wannan tambayar.
Na kasance ina dawowa aikina da magariba ko dare wasu lokutan, kuma adai-dai lokacin nake wanka. Sai wata yar uwata tana yawan hanani, wai ba'ason yawan wanka a irin wadannan lokutan(daga magariba har zuwa dare) saboda lokacine na shaidanu. Shin malam haka abin yake ga jinsin mata da maza, ko kuwa akwai sabani? Nagode
Daga dalibinka N. A ABUBAKAR a zauren fiqhu.

AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Yin wanka bayan magriba ko cikin dare ba haramun bane a addinin Musulunci. Ba'a haramta abu sai ta hanyar kafa hujjah daga Alqur'ani Ko hadisi ingantacce, ko kuma abinda malaman musulunci sukayi istimbatin hukuncinsa daga isharorun nassosi ingantattu.
Malaman fiqhun musulunci basu kebance wani lokaci irin wannan da haramci ba. Misali Imamun Nawawiy acikin littafinsa AL MAJMU'U yana magana akan aikin Hajji, yace "Mustahabbi ne ga Alhaji yayi wanka a kusa da karshen dare a muzdalifah domin tsayawa a Mash'arul Haram da kuma Eidi".
To kaga da ache haramun ne yin wankan dare, da bazai fadi haka ba.
Ash Ashaikh Aliyul Adawiy Almalikiy (rahimahul Lah) yana magana akan wankan janabah, yace "Yafi kyau ga mutumin dake da niyyar yin azumi yayi wankan janabarsa tun cikin dare (wato yafi kyau yayi wanka kafin hudowar alfijir).
Kaja kunnen 'yar uwarka cewa taji tsoron Allah ta dena yiwa Allah karambani. Ba'a cewa abu kaza haramun ne ko halal fache sai da hujjah tabbatacciiya daga Alqur'ani ko sunnah, ki sauran hanyoyin da Malamai ke bi wajen tsagar hukunci daga nassi.

WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)