HUKUNCIN YIN SALLAH DA TUFAFI MAI HOTUNAN MUTANE KO DABBOBI
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. Menene hukuncin yin sallah da riga mai hoto ko atamfa mai zanen tsuntsu?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salam. Ba ya halasta mutum ya yi sallah da tufafin da ke É—auke da hotuna ko zane-zanen abubuwa masu rai, kamar mutane ko tsuntsaye da sauransu, malamai suna kafa hujja da hadisin da Annabi ï·º ya ce: "Mala'iku ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai hoto ko kare".
Bukhariy 3226, Muslim 2106.
Idan wanda ya yi sallah da tufafi mai ɗauke da hotunan rayayyun abubuwa bai san hukuncin hakan ba, to babu komai a kansa na laifi, idan kuwa ya sani, to sallarsa ta yi, sai dai yana da zunubi a mafi ingancin ɗaya daga cikin maganganun malamai Allah ya yi masu rahama, amma daga cikin malamai akawi masu cewa sallar sa ɓatacciya ce saboda ya yi sallah a cikin haramtaccen tufafi.
Duba Majmu'u Fatáwá na Ibn Uthaimeen, mujallad na 12, shafi na 360.
Harwayau kuma, Nana A'isha ta ruwaito hadisi cewa, Annabi ï·º ya yi sallah da wani mayafi da ke É—auke da wasu alamomi, sai
ya dubi wannan tufafi ɗin sau ɗaya, lokacin da ya sallame, sai ya yi umurni da a tafi da wannan mayafi nasa zuwa ga Abu Jahmin a karɓo masa mayafin Abu Jahmin, ya kuma ce:
"Lallai wannan mayafi shi ne ya É—auke mani hankali ga sallata".
Bukhariy 373, Muslim 556.
Saboda haka ya zama wajibi ga mai sallah ya qaurace wa duk wani nau'in tufafi da zai riqa É—auke masa hankali a lokacin da yake sallah.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
