ANNABI DA SAHABBANSA // 012



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

      ANNABI DA SAHABBANSA // 012
.
_Dan Lokaci Kadan Da Yin Wancan Yaqi Na Fujjar Aka Sami Qawance A Wata Mai Alfarma Wato Zulqida, Akan Kira Shi Da Qawancen Fuduul, Wato Halful-fuduul, An Yi Masa Wannan Laqabin Ne Kasancewar Fadal Guda Uku Da Suka Yi Gaggawar Amincewa Da Qawancen, Wato Fadal Bn Fadála, Fadal Bn Wadá'a Da Fadal Bn Harith, Qabilun Quraish Ne Suka Nemi A Yi Hakan._
.
_Wato Banu Hashim, Banul Muttalib, Asd Bn Abdil Uzza, Zuhra Bn Kilab Da Taim Bn Murra, Suka Taru A Gidan Abdullah Bn Jad'anil Taimiy, Sabo Da Girmansa Da Shekarunsa, A Kan Cewa Duk Inda Aka Cuci Wani A Cikinsu Ko A Wajensu Za Su Taimake Shi Har Sai An Dawo Masa Da Kayansa, Annabi Saw Ya Halarci Taron, Bayan Ya Sami Annabci Yake Cewa: "Na Halarci Qawancen Gidan Abdullah Bn Jad'an, Ban Sha'awar Wani Abu Sama Da Shi, Da A Ce Za A Sake Kirata Irinsa A Muslunci Da Na Amsa"._
.
_Wannan Qawancen Ya Kawar Da Duk Wani Qabilancin Da Yake Faruwa A Tsakaninsu, Dalilinsa Kuwa Shi Ne: Wani Mutum Ne Daga Zubai Ya Zo Makka Da Hajarsa, Sai Aas Bn Wa'ilis Sahmiy Ya Siya Amma Ya Hana Shi Kudin, Sai Ya Je Wajen Magoya Bayansa Irin Su: Abduddar, Makhzuma, Jumha, Sahama Da Adiyya Amma Suka Yi Qememe, Sai Ya Hau Dutsen Abu Qais Ya Daga Muryarsa Yana Rera Waqa, Yana Fadin Zaluncin Da Aka Yi Masa._
.
_Nan Ne Zubair Dan Abdulmuttalib Ya Ji, Yake Cewa "Don Me Aka Bar Wannan?" Shi Ne Ya Hada Banu-banuncan Da Muka Fadi A Qawancen Fadul Suka Warware Qawancen Farko Da Ya Sa Suka Yi Watsi Da Shi, Sannan Suka Yi Amfani Da Qawancen Baya Suka Amso Masa Haqqinsa._
.
_Taqaitacciyar Rayuwar Annabi Saw Da Sana'arsa, Za A Iya Cewa Annabi Saw Bai Da Wata Sana'a Guda Daya Lokacin Da Yake Wannan Shekarun, Sai Dai Ruwayoyi Daban-daban Sun Nuna Cewa Ya Riqa Kiyon Tumakin Banu Sa'ad Lokacin Yana Hannunsu, Sannan Kuma Ya Yi Wa Makkawa Kiwo Suna Ba Shi Abin Hasafi, Sai Kuma A Shekara Ta 25 Ya Tafi Sham Da Hajar Khadija Ra Don Kasuwanci, Khadija Bnt Khuwailid 'yar Kasuwa Ce, Kuma Ta Fito Ne Daga Babban Gida._
.
_Koda Yake Ba Da Kanta Take Zuwa Ba Amma Takan Yi Hayan Mutane Kuma Ta Biya Su, To Da Ta Sami Labarin Annabi Saw Kasancewar Ya Taba Zuwa, Sannan Ta Ji Gaskiyarsa Da Ruqon Amanarsa, Sai Ta Nemi Ya Tafi Da Dukiyarta, A Kan Cewa Za Ta Ba Shi Sama Da Abin Da Take Ba Sauran, Ta Hada Shi Da Wani Dan Gidanta Sunansa Maisara, Haka Suka Fita Tare._
.
_Yayin Da Suka Dawo Makka Khadija Ta Ga Yadda Dukiyarta Ta Habaka, Sannan Maisara Ya Ba Ta Labarin Duk Abubuwan Da Ya Gani, Masamman Na Kyawawan Dabi'u, Karamci, Tunani Mai Kyau, Gaskiyar Magana Da Kamewa, Sai Take Ganin Ta Tsinci Dami A Kala, Ta Manta Da Duk Manyan Mutanen Da Suke Nemanta Da Sarakuna, Ta Sami Aminiyarta Wato Nafisa 'yar Maniyya Ta Nemi Da Ta Qyasa Masa In Zai Yarda, Aka Yi Sa'a Annabi Saw Ya Amince, Kuma Ya Yi Magana Da Baffanninsa Suka Sami Baffan Khadija, Suka Nema Masa Ita._
.
_Bayan Dan Wani Lokaci Aka Daura Auren A Gaban Banu Hashim Da Manyan Mudar, Dududu Bai Wuce Wata Biyu Da Dawowarsa Daga Sham Din Ba, Sadakinta Kenan Amaren Raquma Guda Ashirin, Dangane Da Shekarunta Kuwa Duk Mun Tafi A Kan Cewa 40 Ne, Wasu Malamai Sun Yi Ta Kawo Hujjoji Da Za Su Nuna Cewa Ba Ta Kai Hakan Ba, To Amma Su Ma Ba Su Tantance Ba, Shi Ya Sa Na Dogara Da Wanda Yake Hannuna, Na San Dai Babbar Mace Ce Kuma 'yar Dangi, Ga Dukiya Ga Hankali, Ita Kadai Ce Ta Zauna Tare Da Annabi Saw Ba Kishiya Har Allah Sw Ya Amshi Ranta._
.
_Duk 'ya'yan Da Annabi Saw Yake Da Su Nata Ne Ban Da Ibrahim, Ta Shekara 25 Tare Da Shi, A Sauran Shekarun Ne 13 Ya Auri Sauran Matan Wato Su 10, Danta Na Farko Alqasim, Shi Ya Sa Ake Wa Annabi Saw Alkunya Da Abulqasim, Sai Zainab, Ruqayyah, Ummukulthum, Fatima Sai Autansu Abdullah Wanda Ake Masa Laqabi Da Tayyib Ko Tahir, 'ya'yanta Maza Duk Sun Rasu Suna Qanana, Matan Ne Dai Suka Girma Suka Yi Aure Suka Hayayyafa, Amma Duk Sun Rasu Sun Bar Annabi Saw In Ba Fatima Ra Da Ta Rasu Bayansa Da Wata Shida Ba._
.
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)