Sahabban Annabi (ﷺ) Zababbu Ne Cikin Wannan Al'umma:



Ramadaniyyat 1442 [28]

Dr. Muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Sahabban Annabi (ﷺ) Zababbu Ne Cikin Wannan Al'umma:
_________________________________

"Zababbun wannan al'umma su ne sahabban Annabi (ﷺ). A cikin duka wannan al'umma babu wasu wadanda suka fi sahabban Annabi (ﷺ) hadin kai a kan shiriya da addinin gaskiya wanda Allah ya aiko Annabinsa (ﷺ) da shi. Babu kuma wasu wadanda suka fi su guje wa rarrabuwar kai da sabani.
Duk wani abu da za a fada a kansu na kasawa ko laifi, to idan aka kwatanta shi da na wasu cikin wannan al'umma, to nasu bai taka kara ya karya ba. Kamar yadda idan da za a kwatanta aibin da ke cikin wannan al'umma da wanda yake cikin sauran al'ummu, to na wannan al'umma ba komai ne ba.
A inda ake samun kuskure shi ne, yayin da mutum zai rika ganin bakin digo a cikin farar takuwa, amma ya kasa ganin bakar taguwa mai dauke da farin digo a jikinta. Babbu shakka wannan jahilci ne da zalunci".
Ibn Taimiyya, Minhajus Sunna, juzu'i na 6, shafi na 367.

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)