ANNABI DA SAHABBANSA // 088


ANNABI DA SAHABBANSA // 88
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Bayan yaqin Uhud ne Yahudawa suka fara ganin gazawar musulmai, don dimbin asarar da musulman suka yi ta rayuka a hannun wadan da Yahudawan suke ganin sun fi qarfinsu nesa, kuma musulman ba su iya yin komai ba, sai suka ture alqawuran da aka yi da su a baya, suka fito da duk abin dake boye a cikin zukatansu, suka fara magana kai tsaye cikin sirri tsakaninsu da mushrikai da kuma munafuqai, suka ci gaba da gudanar da harkokinsu wanda ba zai taba zama alkhairi ga musulman ba.
.
Duk sun san halin yaqin dake tsakanin musulman da kuma mushrikan, wannan cin amana ne, duk da haka Annabi SAW ya yi haquri da su, har sai da suka yi yunqurin kashe shi gaba daya, hakan ba ya nufin kashe shi a shi kansa, gamawa ce da daular muslunci wanda hanqoron da mushrikan Makka tun dadewa suke matuqar buqata kenan, yanzu dole a koma wancan alqawari da suka rattaba hannu a kai don karbar hukuncinsu daidai da shiri'a.
.
Abin da ya faru shi ne: Annabi SAW ya fita cikin wasu 'yan sahabbansa zuwa wurinsu don tattauna yadda za a yi a biya diyyar mutum biyu dinnan na Banu Kilaab da Amr bn Umayyal Damriy ya kashe, wanda dama akwai wannan cikin yarjejeniyar da aka yi, suka ce ba matsala za su bayar, amma "Abu Qasim ka dan zauna a nan har mu kammala hada abubuwan" Annabi SAW ya sami wani wuri jikin wani gini ya zauna yana jiransu.
.
Sauran sahabbansa kamar Abubakar, Umar, Aliy da dai wasu RA suka zauna tare da shi, su kuma Yahudawan suka fara wasu 'yan gane-gane har dai shaidan ya taimaka musu wajen tsara yadda za su kashe Annabi SAW, suka ce "Wa zai dauki wannan dutsen niqan ya hau gininnan ya sako masa a kai ya kwankwatse shi?" Shedanin cikinsu wato Amr bn Jahash ya ce zai iya, Salaam bn Mashkam ya ce "Kun san Allah kar ku yi"
.
Ya ci gaba da cewa "Don wallahi za a gaya masa duk abin da kuke kintsawa, kuma zai yanke alqawarin dake tsakanimmu da shi" da yake sun riga sun yi niyyar zartarwa kawai sai suka ci gaba abinsu, ilai kuwa, Jibril AS ya sakko ya zayyana wa Annabi SAW komai, Annabi SAW ya tashi cikin gaggawa ya nufi Madina, sahabbansa suka bi shi da sauri suna cewa "Ka miqe ba mu ma sani ba! Ko Yahudawa sun yi wani abin ne?" Annabi SAW ya tura Muhammad bn Maslama da saqo ya gaya musu.
.
Ya ce "Ku tattara qwanku da qwarqwatarku ku bar Madina, na ba ku kwana 10, duk wanda na samu bayan haka zai baqunci lahira" Yahudawa dai ba su da wata mafita dole su bar Madina, sai suka zauna na wadansu 'yan kwanaki, amma sai Abdullah bn Ubay ya aika musu da cewa "Kar ku bar gidajenku, ina da kusan mutum 2,000 zan turo su su shugo tare da ku, sai dai ku mutu gaba daya, 'yan uwanku Banu Quraiza da qawayenku na Larabawan Gatfaan duk za su shugo a yi da su" 
.
Kenan zancen ya koma yaqi na masamman, ba mutanen da za a iya yin sulhu da su ba ne, tabbas Yahudawa bisa wannan alkawari sun sami natsuwa, Qur'ani suratul Hashri ya yi bayanin wannan alqawari da munafuqai suka yi musu, wanda ya sa suka qi bin umurnin da Manzon Allah SAW ya ba su, har da wannan shugabansu Huyay bn Akhtab ya sami qarfin gwiwar aika wa Annabi SAW da raddi yana cewa "Ba za mu bar gidajemmu ba, ka yi duk abin da za ka iya"
.
Kar a manta su 'yan share wuri zauna ne, ba qasarsu ba ce, sun mamaye wuri suna ta shuka tsiya an ce su bar wurin sun ce ba za su bari ba sai dai duk abin da za a yi a yi, wannan abu ya yi matuqar damun musulmai, don babu sakankancewar yaqin zai haifar da da mai ido, suna da masu mara musu cikin Larabawa, kuma zahiri suna da qarfin gaske wanda yin sarandarsu abu ne mai matuqar wahala, ka ga dole abin ya dami musulmai, sai dai da jarabawar da ta sami musulmai ta kisar manyan malamai ta tayar wa da sahabbai hankali.
.
Wannan kisar ta sanya wa kowa qin kafuri, masamman da yake ta yaudara aka kashe su wanda halin Yahudawan kenan kuma, don haka ba wata makawa sai an gwabza, da amsar Huyay ta riski Annabi SAW sai ya yi kabbara, sahabbansa su ma suka yi, aka tashi kowa ya yi damara, Annabi SAW ya ba wa Abdullah bn Umm-Makhtum tsaron gari, Aliy RA ya dauki tuta ya isa can, da zuwa ya mamaye su, Banu Nadeer suka koma cikin ganuwa suka fara harbo kibau da duwatsu, ba shakka dabinansu da gonakinsu sun taimaka musu wajen haka, Aliy RA ya sa aka yanke su gaba daya aka qona.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)