Hrithik Roshan @ 48

Hrithik Roshan Yana cikq shekaru 48-yau a duniya domin ganin an farantawa masoyansa da wannan special birthday da akeyi ayau, jarumin da kansa ya ɗora asalin fita ta farkO tasa daga Qayataccen shirinsa da zai fito anan gaba da aka bawa wannan film ɗin suna kamar haka 👉 Vikram Vedha akan shafin sada zumuntarsa na Instagram ya ɗora wannan fita ta farkon inda zamu gansa zai fito da wata character, ta 'Vedha'. Vikram Vedha ya kasance shiri mai ɗauke da launi da salOn neo-noir action thriller film. Neo-noir ya kasance duk wani shirin Kapcen film da yake ɗauke da labari mai Qarfin gaske wanda yake da alaƙa da wani shuɗanɗan lokaci tun bayan afkuwar yaƙin duniya na biyu daga bigiren lardin United States—ataƙaice tun daga wajen 1945 zuwa 1960. Daga yaren duk Film mai irin wannan salon sun kirawosa da "black movie" ko kuma "dark movie" . Wannan film an shirya sakinsa acikin September 30 acikin gidajen kallo wato cinemas. Jaruman cikin shirin sun haɗa da Hrithik Roshan, Saif Ali Khan da kuma Radhika Apte dukkansu zasu taka muhimmiyar rawa cikin wannan kapcen. Hrithik Roshan ya fara fitowa acikin shirin Bollywood nasa na farko da wani Gawurtaccen shiri maisuna Kaho Naa.. Pyaar Hai acikin shekara ta 2000. Inda yanzu zamuga jarumi Hrithik acikin shirin nasa nagaba maisuna Vikram Vedha.

Vikram Vedha film ne da ya kasance maimaicin wani Tamil hit film, maisuna irin haka. Wanda yake ɗauke da Vijay Sethupathi da kuma R Madhavan Amatsayin jagororin shirin. Wannan film gaba ɗaya dai ya kasance maimaicin labarin wata shikaya ta India maisuna Vikram aur Betaal, Inda labarin wannan shirin ya kasance akan tsangayar wani police officer maisuna 👉 Vikram wanda jarumi Saif Ali Khan yake da yunQuri da aniyar neman wani uban daba da zamuga jarumi (Hrithik Roshan) Akan Wannan sigar.

Post a Comment (0)