MIJINTA YA SADU DA ITA YAYINDA TAKE HAILA MEYE HUKUNCIN WANKANTA NA JANABA DA NA HAILA?

MIJINTA YA SADU DA ITA YAYINDA TAKE HAILA MEYE HUKUNCIN WANKANTA NA JANABA DA NA HAILA?



:
TAMBAYA❓
:
malam tambayata itace. Macece tana al'ada sai mijinta yakusanceta .toh kafin tafara al'ada sundan kwana biyu basu kusanci junaba.shine tana al'ada mijin yakusanceta.tayi tayi hakuri yace wlh baza iyaba.toh malam meye hukunci wankata na janaba dana al'ada
:
AMSA👇
:
To bayin Allah Babu shakka wannan ya nuna dukkansu basu san girman laifin saduwa yayin haila ba domin da shi mijin yasan girman laifin saduwa da mace a halin haila to da bai rantse cewa shi bazai iya hakura ba, hakanan Itama da tasan girman laifin saduwar yayinda take haila da bazata manta da tambayar hukuncin abinda suka aikata ba. Sabida haka Idan basu sani ba su sani ANNABI MUHAMMADU ﷺ YACE: TSINANNE NE DUKKAN WANDA YAKE SADUWA DA MACE YAYINDA TAKE HAILA KUMA TSINANNE NE DUKKAN WANDA YAKE SADUWA DA MACE TA DUBURA [Abu Dawud:Tirmizi:Ibn Maja] Kai a wani hadisinma Annabi Muhammadu ﷺ cewa yayi Duk wanda yake saduwa da mace a lokacinda take haila Ya kafircewa Abinda aka saukarwa Annabi Muhammadu ﷺ .
..
Sabida haka lallai shi mijin yaji tsoron Allah kuma yayi gaggawan tuba ya nisanci saduwa da matar yayinda take haila matukar dai bayason ya kasance cikin mutanan da Annabi ﷺ ya tsinewa sakamakon saduwa da matansu a lokacin haila. Sannan kuma zeyi kaffara ta zunubinda ya aikata ta hanyar sadakar da kuɗin da yayi daidai da 'kimar dinare ɗaya idan a farko farkon hailar ya sadu da ita, idan kuma karshe karshen hailar ya sadu da itan sai ya sadakar da kuɗin da yayi daidai da 'kimar rabin dinare ɗaya Wannan shine kaffararsa.
..
Ita kuma idan tilasta mata yayi ma'ana ta karfi yayi mata to Hakika ita bata da laifi. idan kuma biye masa tayi wato son zuciyarta itama tabi to Wallahi itama ina jiye mata tsoron kar ta auka cikin matan da Allah zaiyi fushi dasu, Sabida haka lallai ta sani ba'a yiwa miji biyayya wajen sa'bawa Allah.

Dangane da Hukuncin wankan kuma wanka biyune zatayi wato wankan haila da wankan janaba
..
Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH


Post a Comment (0)