MUMININ DA YAKE CAKUƊUWA DA MUTANE...

MUMININ DA YAKE CAKUƊUWA DA MUTANE...


💫 Babu alkhairi sosai ga muminin da yake nesantar mutane, kuma baya yin haƙuri idan sun cutar dashi.

💫 Mumini na ƙwarai baya nesantar mutane, kuma baya gaza yin haƙuri idan sunyi masa abinda ya ɓata masa rai, mumini na ƙwarai yakan yi mu'amala da mutane cikin girmamawa da kare haƙƙin ɗan-adam-taka, baya jin cewa shine kaɗai mai imani, kuma baya raina mutane abisa ayyukan laifukansu, yakan fahimtar dasu sharrin ayyukan saɓonsu cikin hikima da girmamawa.

🌴 An karɓo daga ɗan umar Allah ya ƙara masa yarda yace: lallai Manzon Allah ﷺ, yace: "muminin da yake yin tarayya da mutane kuma yayi haƙuri abisa cutarwarsu, shi yafi girman lada fiye da muminin da baya yin tarayya dasu kuma baya yin haƙuri abisa cutarwarsu"
📒 Sunan Ibn Majah (4032)

Post a Comment (0)