SHIN DAGASKE ANNABI S.A.W YAFAƊI HAKA..?

SHIN DAGASKE ANNABI S.A.W YAFAƊI HAKA..?





TAMBAYA❓
:
Assalamualaikum warahamatullah barkan da warka malam ya aiki to Allah ya taimaka ya bada sa'a Allah yasa ka Gama da duniya lfya amin
Shine malam wannan ya tabbata daga manzon S.A.W ne ko ya abun yake
I🙏SIRRIN GIDAN ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM🙏

Don allah idan kakaranta kaƴi share a gorups uku

Duk wanda yake cikin kunci Lamarinsa ya tsaya chak kumaa yana so Allah yabuda Masa toh ga siirii Mai girman gaske.

Wallahi Wallahi Wallahi ko kana shakku kajarraba zakaga Lamunin Annabi saw (Innamal a'amalu bin niyat)

SIRRIN FATIHANE BABU YAWA SAI ZAFI

Ga yanda akeyin aikin kwana bakwai zakayi indai kayi jalabine na wata daya

Ana fara sirrinne duk lahadin farkon watan Muslunci 

 Ranan Lahadi zaka biya FATIHA kafa 70
 Ranan Litini zaka biya FATIHA kafa 60
 Ranan Talata zaka biya FATIHA kafa 50
 Ranan Laraba zaka biya FATIHA kafa 40
 Ranan Alhamis zaka biya FATIHA kafa 30
 Ranan Juma,a zaka biya FATIHA kafa 20
** Ranan Asabar zaka biya FATIHA kafa 10

Iyakanshi kenan amma duk wata akeyi wallahi indai kayi sai kaga canji fiye da watan da kafito wajan budi da samun kudi da sauransu

Kaidai kayi kai kuma kaga lamanin Annabi s,a,w 
Wannan munba masoya Annabi domin Allah yadauke mana wannan kuncin da ake ciki.

Ya Allah duk wanda yatura wannan post cikin group uku kanuna masa Annabi Muhammad (((SAWW))) acikn mafarkinsa ameen
:
AMSA👇
:
 Wa Alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu


Imamu Bukhari da Imamu Muslin sun Ruwaito wani hadisi wanda Annabi (saw) Ke gaya mana cewa ƙarya takan kai mutum wuta.
Annabi (Saw) yana cewa, “Ku kiyayi ƙarya, domin ita ƙarya tana jan mutum zuwa saɓon Allah, shikuwa sabon Allah yana kai mutum zuwa ga wuta, hakika mutum ba zai gusheba
yana ƙarya harsai an rubutashi awajen Allah cewa shi maƙaryaci ne” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito sh.
.
Qarya babban zunubi ce wadda ayoyi da hadisai sukayi magana akan haramcinta da kuma narkon azabar da za'ayiwa makaryaci. Musamman ma yiwa Annabi saw ƙarya.
An Ruwaito hadisi Cewa, Annabi Saw yana Cewa, “Duk wanda yayi mini karya da gangan, toya tanadi mazauninsa acikin wutar jahannama” Bukhari da Muslim.
.
Wannan shiriritar bashida Alaƙa da zancen Annabi Saw, dan haka kuyi watsi dashi wani ƙaton jahilin ne da shaiɗan yayi masa huɗuba yazauna yatsara 

Allah ya kiyayemu

DAGA ZAUREN
📘 HISNUL Muslim 📘


Post a Comment (0)