WANI SALLAH KE KAINA BAYAN DAUKEWAR JININ HAILA?

WANI SALLAH KE KAINA BAYAN DAUKEWAR JININ HAILA?
:


*TAMBAYA*❓
:
Aslm dafatan antashi lfy Allah Ya taimaka, tambayata shine yaya ake gane daukewan haila idan yatafi dasafe wani sallah akebinka inkuma dayammane koda daddare wani sallah zaka biya bissalam
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumussalam Warahmatullah Wabarakatuh
To a yanda na fahimci wannan tambayar ba tana tambaya akan alaman daukewan jinin bane. Kamar tambayar akan wani Sallah ne yake kanta bayan tayi wanka.?

To Sallan da zakiyi bayan kinyi wanka shine Sallanda kikayi tsarki a cikin lokacinsa (wato jinin ya ɗauke koda bakiyi wankaba). Misali ya dauke da safe bayan sallan asuba, amma rana bata fitoba. Kuma adaidai wannan lokacin inda ace kina cikin tsarki, zaki iya yin cikakken raka'a ɗaya rana bata fitoba, to idan kikayi wanka, zakiyi sallan asuba, koda ace saida rana ta fito kafin kikayi wanka.
Misali ace a raka'a ɗaya na sallan asuba yana kai minti biyar👌🏻 to sai jinin ki ya ɗauke kafin fitowan rana da minti biyar. To sallan asuba na wannan ranan yana kanki dole sai kinyi koda bakiyi wanka da wuriba.
Hakanan idan da yamma ne jinin Ya ɗauke kafin faduwan rana da kamar minti biyar, to in kikayi wanka sai kinyi la'asar kafin kiyi magriba.
Sannan inda ace jini zaizo miki kafin kiyi Sallan asuba, amma alfijir ya riga ya fito, kecedai bakiyi sallanba, to duk randa kikayi tsarki zaki biya wancan asuba ɗin. Haka kowace sallah idan kikayi al'ada a cikin lokacinta ba tareda kin sallacateba. To kinayin tsarki zaki rama wannan Sallan.

Wallahu A'alam.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)