ANA BIYANA ALBASHI, AMMA BANA ZUWA WURIN AIKI, YAYA HUKUNCINA ?
*Tambaya*
Assalamu Alaikum WarahmatulLAH? Barka da dare Dr dafatan kawuni lafiya Allah Yasa haka Shaikh Inada wata Tambayane ataimakamin da amsa. Dr, Matace tana aikin Gwamnati a wata jaha sai kuma barin Jahar ya kama su ita da mijinta ma'ana suka tashi kwata-kwata daga Wannan Jahar sai ya zama bata zuwa aikinta amma kuma Ana bata Salary duk wata amma Principal din makarantar da take aiki yana sane shi ya amince mata ta tapi sai kuma wani Ma'aikacin ma'aikatar Ilmi to amma ma'aikatar ba ta da masaniya to Dr Yaya kudin datake karba duk wata Ya halatta taci gaba da karba ko ta daina karba? don Abun yana damunta tana ta tunanin abun koda yaushe. Ataimaka min da Amsa Dr. Bissalaam
*Amsa*
Wa alaikum assalam,
Bai halatta ta ci ba, saboda albashi ana bayar da shi ne ga wanda ya yi aiki, halattawar da principal ya yi mata ba zai ba ta damar cin kudin ba tun da ba mallakarsa ba ne, kudin al'uma ne mabukata.
Hukuncin yana zagayawa ne tare da sanuwar dalilinsa ko rashinsa.
Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi a rai,kuma ka ji tsoran kar mutane su tsinkayo kai, kamar yadda hadisi ya tabbatar.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR.JAMILU YUSUF ZAREWA*
22/02/2017.
*📚Irshadul Ummah.*