BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA

BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA ! !


Tambaya:
Assalamu alaikum, malam INA da wata tambaya shin menene hukuncin yin bacci bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!

Amsa : 
To malam babu wani hadisi ingance wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, saidai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi s.a.w. idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta : 670, kuma Annabi s.a.w yana cewa : "Allah ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta : 1212, kuma ya kyautata shi.

Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai albarka, wanda bai dace da bacci ba, wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi s.a.w. yake so ya aika, yakan aikata ne a farkon yini saboda albarkar lokacin.

Wasu daga cikin magabata, sun karhanta yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a Musannaf dinsa 5\222.

Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko kosuwanci a irin wannan lokacin.
 
 Allah ne mafi sani .

*Dr Jamilu Zarewa*
.

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)