BA ZATA RAYU BA SAI TA SAYI ISKAR DA TA KE SHAKA KOWANNE SAKAN, A HAKA AKA KORETA DAGA GIDAN DA TAKE HAYA.

BA ZATA RAYU BA SAI TA SAYI ISKAR DA TA KE SHAKA KOWANNE SAKAN, A HAKA AKA KORETA DAGA GIDAN DA TAKE HAYA.


Na san ba za ku manta da Aisha baiwar Allah da ke rayuwa akan iskar da take SHAKA ta inji ba, wanda kullum sai ta siya wannan iskar, watanni baya mun nema mata taimako gurin bayin Allah, wanda ya sa ta dan samu sauki kadan, amma daga baya abubuwan suka kara dawowa, domin duk watan duniya sai ta sayi iskar sama da Dubu dari biyu ban da magunguna, kullum na tuna Aisha da yadda ta ke rayuwa sai na yi hawaye na godewa ubangiji. 

A wannan hali da Aisha ke ciki masu gidan da ta ke haya suka ce ta tashi, ba ta da inda za ta koma kuma ba ta da mai tallafa mata, daga lokacin da aka ce Aisha ta tashi ciwonta ya karu bata iya bacci sai kuka da damuwa, domin tace idan ta bar unguwar nan da ake samun wuta za ta iya rasa rayuwarta, domin da wutar nefa injinan ke aiki, idan ba haka ba sai dai a kunnna injin Generator ya wuni, da me za ta ji, da kudin Iska ko da na fetur ko karar Generator?😭😭😭

Duk watan Allah sai ta sayi iskar da ta ke SHAKA ta sama da Dubu Dari biyu, ga kuma yaranta biyar da ta ke kula da cin su da shansu da kudin makarantarsu.

Yan'uwa ku taimakawa Aisha da gurin zama a garin Kaduna inda ta ke zaune, musamman bangaran da ake samun wuta, sannan ku taimaka mata da yadda za ta ci gaba da siyan iskar nan, domin a halin da ta ke ciki a haka ta ke sana'ar online kala-kala domin ta samu abun da zata kula da kanta da, ku taimaka mata kar kuma ta samu ciwon zuciya saboda damuwa bayan wancan ciwon.

Ga Wanda kuma za su taimaka mata saboda Allah za su iya tura taimakonsu ta account Din Aishan wato;

Acc no: 0232349741
Acc name: Aisha Aminu.
Bank name: GT.

Ga masu neman karin bayani ko bukatar ganinta kaitsaye, za su iya kiran lambar wayarta. 08160064471.

Allah ya ba ku ikon taimakawa Aisha ko da Naira dari ce, sai ku ga an hada mata kudin da zata samu gurin zama, idan Allah ya sa aka dace ma sai a saya mata nata gidan ko mu samu wani ya bata kyauta Insha Allah, ku tayamu yada wannan posting din don Allah har Allah ya sa a dace, mungode.
Post a Comment (0)