RABA UWA DA ĐANTA

RABA UWA DA ĐANTA


Tambaya:---- 

 Allah ya kare malam ya Kuma gafartawa iyaye amiin.malam ga tambayata kamar haka nayi aure na haifi yara biyu Amma na rabu dashi ya kwashemin yata Kuma yan uwanshi sun hanani zuwa in ganta shin malam inada aibu ko alhaki kokuma wani laifi yanzu shekara 3 bangantaba

Amsa:-- 

1) Babu kyau a raba uwa da đanta, mai yin hakan za a raba tsakaninsa da masoya a ranar Qiyama. [TAKHRI'JUL MISHKAT; 3361, I'ILA'MUL MUWAQQI'IN; 2/221]
.
.
2) Mace ta na da izinin zuwa ganin yaranta a bayan mutuwar aure, idan babu kebanta da tsohon mijinta. 

[FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 20/19]
.
.
3) Babu laifi musulmi ya kai kara a kotu idan an kwace ma sa wani hakki, idan babu wata hanyar gyara.

 [FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 23/502]

Amsawa:--- Sheikh Abdurrazaq Yahya Haifan
.
.
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a bibiye mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram:---- https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)