​​HUKUNCIN TARA MUTANE AYI ADDU'A YAYIN TAREWA A SABON GIDA?​​

​​HUKUNCIN TARA MUTANE AYI ADDU'A YAYIN TAREWA A SABON GIDA?​​



TAMBAYA❓

Assslam alaika warahamatullah malam INA maka fatan alkairi don Allah malam menene hukuncin kiran mutane ayi addu'a koh saukar Al'kurani lokacin da zaa tare a sabon gida kokuma zaa bude shago?

AMSA👇

Wassslam alaika warahamatullah wabrakatuhu ina godia da fatan alkairi tabbas akwai dabi'ar da mutane suke yayin da suka gina gida ko kuma zasu bude shagon kasuwanci sai kaga an kira mutane ko gardawa a sanyasu suyi addu'a kafin a tare a gidan.
Da farko dai yan uwa yana da kyau mu gane cewa addu'a dai ibada ce kuma ana bukatar addu'a ako ina, amma ana addu'a ne bisa tsarin yadda shari'a tace ayi babu inda shari'a ta tsara cewa idan kayi sabon gida ko kuma shago kaje kayi gayyar mutane ayi addu'a ba, ko kuma saukar Alkur'ani ba kafin ka shiga gidan.
Annabi S.A.W ya koyar damu addu'ar da zamuyi itace:
​​A'UZU BI KALIMATULLAHI TAMATI MIN SHARRI MA KALAKA).​​
Haka Annabi S.A.W yace duk wanda zai sauka a wani waje sabo ko tsoho to yayi wannan addu'ar wannan shine abinda Manzon Allah S.A.W ya koyar damu amma baice mu hadu a sauke Alku'ani ba ko kuma ayi gayyar addu'a ba duk da cewa saukar Alkurani abune mai kyau hakama addu'a amma ana yinsu ne a inda shari'a tace ayi
Misali karatun Al'kurani abu ne mai kyau amma bazai yiyu don mutum yana sha'awar karatun ba kawai yayi ta karanta Alkur'ani a sujjada ba ko kuma ruku'u, saboda ba wajansa bane domin komai shari'a ta kebance inda zaayi.

Allah shine mafi sani

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.


Post a Comment (0)