KADA KAYI GABA DA MUSULMI

🤔 KADA KAYI GABA DA MUSULMI 🤔


🍁 Abin mamaki!, yau gaba da nuna ƙiayayya ga juna ta zama ruwan dare ga musulmai, sai kaga waɗansu wai ƴan-uwa ne, amma wani abu mara dalili ya haɗasu yin gaba da juna, kowa yana jin haushin kowa.

🍁 Wasu gabar tasu takan samo asali ne daga bambancin ra'ayin siyasa, ko Banbancin ra'ayin ƙwallon ƙafa, dadai makamantansu, wanda kuma yin hakan kuskure ne, kuma babban laifi ne a musulunci.

🍁 Kai wasu ma zaka ga gidansu ɗaya, uwa ɗaya ko uba ɗaya, amma wai yau wani abin duniya yasa suna yin gaba da junansu, subhanallah!. 🙆🏻‍♂️

🌴 Manzon Allah ﷺ, yace: *"baya halatta ga musulmi ya ƙauracewa ɗan-uwansa fiye da kwana uku, zasu haɗu (amma) sai wannan ya kauda kansa, wancan ma ya kauda kansa (suna kawar da kawunansu ga junansu), to mafi alkhairin cikinsu, shine wanda ya fara yiwa ɗan-uwansa sallama"*
📒 Bukhari Da Muslim suka ruwaito

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)