💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi 03

*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*


*✨سؤال وجوب في أحكام الصيام.*

Wallafar:
Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.
.
.
Da sunan Allah, Mai rahama Mai jin 'kai.

(2) KAMEWA DAGA CI DA SHA:

Tambaya III: A wasu taswirorin, muna ganin suna rubuta; minti 10 ko 15 da fitar dare, shin wannan sunnah ce ko bidi'a? 

Amsa: Wannan bidi'a ce, ba shi da asali a sunnah. Allah (SWT) ya ce:

*”...وَكُلُواْ وَاشْرَبُواْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّواْ الصِّيَامَ إِلَى الَّليْلِ...“*

Ma'ana: *“...Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa´an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare...”* (Suratul Baqarah: 187).

Annabi (ﷺ) ya ce: *“Lallai ne, shi Bilal yana kiran sallah ne cikin dare (kafin fitowar alfijir), a wannan lokacin, ku ci ku sha har sai kun ji kiran sallar Ibn Ummu-Maktum, domin hakika, yana kiran sallah ne kaďai bayan ketowar alfijir.”* Bukhari da Muslim. 

Saboda haka, ke6ance wani lokaci na daina cin abinci wanda ya sa6a wa fadin Allah (SWT) da manzonSa wuce gona da iri ne. Annabi (ﷺ) ya ce: *“Ku lura! Masu wuce gona da iri sun halaka, masu wuce gona da iri sun halaka, masu wuce gona da iri sun halaka”.* (Muslim: 2670).

Wallahu A'lamu.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)