YA HALATTA MUTANE BIYU SU KWANA A BARGO DAYA?

YA HALATTA MUTANE BIYU SU KWANA A BARGO DAYA?


 *TAMBAYA* ❓
:
Assalamu alaikum Meye hukuncin mutane biyu su kwana a bargo daya.
:
 *AMSA* :👇
:
Amsar wannan tambaya tana a karkashin wannan hadisi na Abdullahi ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu).

`ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﻣُﺮُﻭﺍ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩَﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﺳَﺒْﻊِ ﺳِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﻋَﺸْﺮٍ ﻭَﻓَﺮِّﻗُﻮﺍ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﻀَﺎﺟِﻊِ.
( ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏(495) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ"

An karbo daga Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu) yace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yace; Ku umarci 'ya'yanku da suyi sallah idan sunkai shekara bakwai. Kuma Ku dakesu Idan sunkai shekara goma (basa yin sallah), kuma ku rarraba su a makwancinsu (a raba musu shinfida idan sun kai shekara goma).
(Abu Dawuda, 495). Albani ya inganta shi a Sahih Abi Dawuda.

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
 ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺟﺎﻧﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﺼﺒﻲ ﺃﻭ ﺍﻟﺼﺒﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ ﻭﺃﺧﺘﻪ ﻭﺃﺧﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻀﺠﻊ.
"ﺭﻭﺿﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺒﻴﻦ ‏( 7/28 )"

Imam Nawawi (rahimahullah) yace
Baya halatta ga namiji ya kwanta tareda namiji (a shimfida guda), ko kuma mace ta kwanta tareda mace (a shimfida guda), koda dayansu yana a gefe daya na shimfidar. Idan yaro ko yarinya suka kai shekara goma, ya zama wajibi a raba yaron (a shimfida) tsakaninsa da Mamarsa, Babansa, yar uwarsa (kanwa ko yayarsa), da dan uwansa a wajen barci. (Dole ne ya rika kwanciya a shifidarsa shi kadai).
Rawdatul taalibeen, 7/28).

Saboda haka bai halatta mutum biyu su kwana a shimfida daya ba idan shekarunsu sun kai goma (10).

Namiji bazai kwanta shimfida daya da wani namiji ba.

Namiji bazai kwana da wata mace wacce ba matarsa ba a shimfida daya. Wannan haramun ne.

Mace bazata kwana da wata mace ba a shimfida daya.

Mace bazata kwana a shimfida daya da wani namiji wanda ba mijinta ba
:
Wallahu A'alamu.
:
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)