AN KORE NI AIKI SABODA HALIN SHAYE-SHAYE.
*TAMBAYA*❓
:
_As-Salamu Alaikum,_
Malam, ina aiki ne sai aka kore ni saboda halin shaye-shaye. Na sake samun wani kyakkyawan aiki irin na-baya, amma kuma aka sake kora na saboda waccan matsalar dai. Yanzu haka na tuba, na daina wancan halin, amma kuma ban samu wani aikin ba. Kuma na ji wai Allaah ba ya ba mutum dama fiye da sau biyu! Ga kuma mates ɗi na duk sun zama manyan mutane. Malam, yaya zan yi?
:
*AMSA*👇
:
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._
[1] Abin da na san Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce shi ne:
*Ka ce: Ya ku bayina, waɗanda suka ɓarna ga kawunansu! Kar ku yanke tsammani daga Rahamar Allaah! Haƙiƙa! Allaah yana yin gafarar zunubi dukkansa. Haƙiƙa! Shi Mai Yawan Gafara ne, Mai Yawan Tausayi.*
_(Surah Az-Zumar: 53)_
Don haka, kome girman zunubinka da yawansa Allaah Ta’aala zai iya yafe maka shi, ya gafarta maka, matuƙar dai ka tuba gare shi tuba na gaskiya, kuma ka bi ƙa’idoji da dokokin da Shari’a ta shimfiɗa a wurin tuban. Shiyasa ma a ayar da ta biyo bayan wannan ya ce:
*Kuma ku komo zuwa ga Ubangijinku kuma ku sallama (miƙa-wuya) gare shi, tun kafin azaba ta je muku, sannan kuma ba za a taimake ku ba.*
_(Surah Az-Zumar: 54)_
Wannan ita ce kaɗai mafita gare ka da sauran jama’ar duniya, tun da dai mutum a duniya ba shi da mafaka ko matsera daga Allaah sai dai ya koma gare shi, kamar yadda Annabi ﷺ ya faɗa a cikin addu’arsa.
[2] Amma dangane da korarka daga aiki saboda ɗabi’ar SHAYE-SHAYE, wannan na daga cikin nason sharrin zunubi ne tun daga nan duniya kafin makoma Lahira. Kuma a iya cewa kai Allaah ya yi maka da kyau, tun da ma har ka iya fahimtar cewa wannan laifin ne ya janyo ake sallamarka daga aikin da ka samu, kuma don haka ka yi gaggawar tuba. Wani ba za a sallame shi ba, sai dai ma kawai a ƙara masa girma! Kuma ko an sallame shi ba zai gane cewa wannan zunubin ko saɓon ne dalilin ba. Don haka, sai kawai ya cigaba da aikata zunubansa a cikin jin daɗi da annashuwa, har sai ya mutu a kan haka, kuma sai Allaah ya kama shi, cikakken kamu.
[4] Rashin samun wani aiki a bayan tuba, kuma da kasancewar _mates_ ɗinka duk sun zama manyan mutane ban da kai, wannan bai nuna cewa Allaah bai karɓi tubanka ba, ko kuma har yanzu yana fushi da kai, kuma wai bai yarda da kai ba. Wajibi ne ka san cewa samun aiki mai kyau ko rashin samunsa ba shi da alaƙa da amincewa ko yardar Allaah Ta’aala ga bawansa. Allaah yana bayar da duniya ga wanda yake so da wanda ma ba ya sonsa daga cikin bayinsa. Amma addini ne ba ya bayarwa sai ga wanda yake so kawai, kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi daga Annabi ﷺ A wurinsa _Subhaanahu Wa Ta’aala_ bayar da arziki ga bawa jarrabawa ne, haka ma rashin bayarwar. Abin dai da ya wajaba gare ka, kamar yadda ya wajaba ga kowa a nan shi ne: Cigaba da yawaita yin addu’a ga Allaah _Subhaanahu Wa Ta’aala_ tare da tawali’u da ƙan-ƙan da kai gare shi da cewa: *Ya ba mu kyakkyawan arziƙi a duniya, kuma kyakkyawan arziƙi a Lahira, sannan kuma ya tsare mu daga azabar Wuta.*
[5] Amma maganar wai Allaah ba ya bai wa mutum dama fiye da sau biyu, ban san wannan a cikin karatu ba. Idan dai har bawan Allaah ya tuba, kuma Allaah ya karɓi tubansa ai shikenan ya zama kamar mara laifi ne. Tun da kamar yadda Annabi ya faɗa: Shi Musulunci yana rushe duk abin da ya gabace shi na zunubi da laifuffuka ne. Wannan maganar kusan a ce ma tana daga cikin masu kangararwa ne, kuma masu sanya wa mutum ɗabi’ar ɗebe tsammani daga samun Rahamar Allaah, wanda kuma ba ɗabi’ar musulmi ba ce.
Allaah nake roƙo da Sunayensa Kyawawa da Siffofinsa Maɗaukaka, Wanda kuma duk rayukan bayi su ke a tsakanin yatsu biyu daga cikin yatsun hannunsa da cewa:
*Ya Ubangijinmu! Kar ka kautar da zukatanmu bayan har ka shiryar da mu, kuma ka yi mana baiwar Rahama daga wurinka. Lallai kai! Kai ne Mai Yawan Baiwa.*
_(Surah Al-Imraan: 8)_
_Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Majlisin sunnah
08164363661
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ