HUKUNCIN NAMIJI MAI DUKAN MATARSA

HUKUNCIN NAMIJI MAI DUKAN MATARSA
:


TAMBAYA❓
:
malan inada tambaya mijina kullum idan mukayi faɗa saiya dinga duka na😥😥😥😥😥😥🙏koyaya na batamai rai sai duka yamae Dani jaka sai idan dare yayi sai yace Yana bukatata sabida ya kasance me bukata malan menene hukuncin wannan auran
Nagayama iyayena sunce yadena duka Amma dukda haka bai bari ba
Malan menene mafita Dan Allah 😥😥🙏🙏🙏🙏🙏
Wlh malan komae kankantar laifi sai duka zagi yaytamun masifa mutane naji 😥😥😥😥😥🙏🙏🙏
Dan Allah menene mafita
:
*AMSA*👇
:
Tabdi! Duk Macen da ta tsinci kanta a gidan namiji mai duka tofa sai tayi hakuri kan hakuri. Domin wani ya mai da kumatun matarsa kamar kumatun wani kato, sai dai kawai kaji ya falleta da mari, ya tadiyeta yayi ta dukanta kamar baiwarsa shi ko kunya ma baya ji.
Yazo a Hadisi Annabi (SAW) Yace "Shin dayan ku baya jin kunya ya duke matarsa kamar yana dukan baiwa, zai duketa da rana sannan ya nemi saduwa da ita a karshen dare shin baku jin kunya". Don haka ba komai bane matar ka zatayi maka kayi ta dukanta, kayi mata targade ka kumbura mata jiki wata ma har tana zuban jini sabo da mugun dukan mijinta. Ba'a kwana biyu ba tare da ya lallasa matarsa ba.
Kadan daga cikin Shawarar da zan baki a nan 'yar'uwa shine, Fushi da zafin zuciya da 'bacin rai shi yake jawo namiji ya daki matarsa, don haka idan yace wance kibar kaza kiyi kokari ki bari, idan yace wance ayi mun kaza yi sauri ki tashi kiyi masa. Ki daure wurin kaucewa abin da zai jawo ya duke ki.
Sannan wani lokaci kace nace shi yake janyo namiji ya kaiwa mace duka, don haka idan yazo yana fada yana zagye zagye kice wane nasan abinda nayi ban kyauta I'm sorry, Allah ya huci zuciyar ka, daga nan kiyi shiru yayi ta fadansa, domin kada yazo garin tanka masa ya faffaleki da mari.
Sannan iya magana, idan mijin ki bahagon namiji ne tofa sai kin iya magana ta yadda da yazo yana fadan nan sai ki kalallame shi da sanyayan kalmomi, kiyi taushi kiyi sanyi ki zama kamar kankara. To idan mai tausayine sai kaga yayi shiru ya daina fadan. Don wasu kwata kwata basu iyawa namiji mai zafi sanyayan kalamai ba.
Sannan ki dagye da addu'a, domin gaskiya rayuwar auren ba zai rinka yi miki dadi ba, tunda wanda ya kamata yasa kiji dadin shine kuma yake kilarki. Ina rokon Allah ya gyara tsakanin ko wacce mace da mijinta mai irin wannan halin. 

WALLAHU A'ALAm

Zaku iya samu wannan group na Facebook da na telegram ta wannan hanyar
TELEGRAM👇🏻
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)