JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 05

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 05


MUSA AS DA FIR'UNAN ZAMANINSA
.
Fir'auna mummunan suna ne ko a wurin musulmai ma bare Yahudawa da ya nemi qarar da su kacokan, asalin sunan fir'auna ba abin qyama ba ne, sunan sarauta ne, tamkar yadda muke kiran jagororin qasar Hausa da sarakuna, na Adamawa mu ce masa Lamido, na Borno kuwa shehu, haka duk wanda ya mulki Farisa wato hambararriyar daular Iran sukan kira shi da kisra, wanda ya mulki rusasshiyar daular Rum sukan ce masa qaisar, na Habasha su kira shi da najashi, na Masar kuma su ce masa fir'auna, kowa na da sunansa na yanka da na sarauta, sai dai mu sunan sarautar ya fi kama mana baki don shi muka sani.
.
Muhammad bn Abdirrazaq Al-Juwaili ya fadi a cikin silsilarsa ta (Fir'aunan Musa) wace yake cewa a watan Disamba 2019: Malaman tarihi da masu bin diddigin falaki sun sami daidaito bayan tattaunawa mai tsawo kan cewa Walid bn Mus'ab shi ake kira da Ramsis na biyu, wato Fir'aunan zamanin Musa AS kenan (Tarikhut Tabari j1 p231, Tarikhul Ya'aqubiy j1 p33) za ka sami tafsirai sama da 30 wadanda suka tabbatar da wannan suna na Walid bn Mus'ab. Fir'auna ya mallaki Masar na tsawon lokaci kuma ya yi qarfi har ta kai ga yana jin cewa ya isa ya kira kansa Allah.
.
Ya addabi mutane da dama masamman Banu Isra'ila wadanda muke fama da su yanzu, ya qasqantar da su fiye da yadda kowa yake zato, wadannan mutane suna da dogon tarihi matuqa, amma an fi tantancewa da cewa asalinsu daga Iraqi suke, domin nan ne Annabi Ibrahim AS ya baro ya dawo yankin Sham, har ya sami yara biyu, dan wajen Hajir wato Isma'il AS shi da mahaifiyarsa aka kawo su Makka don su raya wurin bautar Allah acan, shi kuma dayan wato Is'haq AS yana tare da mahaifiyarsa Sarah, shi ne mahaifin Ya'aqub wanda ake masa laqabi da (Isra'il), shi ma ya sami wannan laqabin ne don ya taba yin isra'i zuwa ga mahalicci kamar yadda yake a tarihinsu.
.
To Ya'aqub shi ne mahaifin Yusuf AS, kenan Yusuf bn Ya'qub, bn Ishaq bn Ibrahim AS, a cikin tsatsonsu ne Musa AS ya taso, shi ya sa ake cewa shi ma daga banu Isra'ila yake, in ba mu manta ba Tarihi ya nuna mana cewa sun bar Palastinu ne tun a zamanin Fir'aunan Yusuf AS, lokacin da shi Yusuf AS din ya sami babban matsayi a gidan fir'aunansa ya aika musu da su taho Misra tare da mahaifinsu, zuwansu Masar suka zauna suka ci gaba da rayuwa anan din, sai dai akwai maganganu masu dukan juna a tsawon lokacin, domin ana cewa tsakanin Musa AS da Yusuf AS shekaru 97 ne kacal.
.
Amma Aliy Jumu'a tsohon shugaban masu Fatawa na qasar Masar ya fadi a wani bayani da ya yi kan talabijin din Qanatul ula cewa "Akwai shekaru daidai har 400 tsakanin Annabi Yusuf AS da Annabi Musa AS, anan ne ya bayyana cewa mutum 200 ne suka baro Palastinu zuwa Masar, yanayin hijira da haihuwa a hankali har yawansu ya kai dubu 70", su ne fa Fir'auna ya saka a gaba da azabtarwa ya riqa kashe 'ya'yayensu maza yana barin mata saboda zalinci da jiji da kai da isa, sun sha nau'o'in azaba a hannunsa kala daban-daban, ga wulaqanci ga bautarwa suka yi haquri har Allah SW cikin ikonsa da buwayarsa ya yi musu ni'ima, ya raba su da wannan qasar ya maishe su sarakuna, manyan mutane masu fadi a ji, ya wulaqanta Fir'auna da Hamana ya qwace mulkinsu suka koma tarihi.
.
Abin tambaya anan: Ina Fir'auna ya samo labarin cewa za a haifi yaro a banu Isra'ila wanda zai zama sanadiyyar rasa mulkinsa? Ni dai tun ina yaro nake jin cewa bokaye suka gaya masa, amma Ibn Kasir ya ce: "Lokacin da Ibrahim AS ya zo Masar Fir'aunan lokacin ya yi qoqarin maida Sarah kuyangarsa qarfi da yaji Allah ya qwace ta, shi ne daga baya Ibrahim AS ya yi wa dansa bushara da cewa a tsatsonsa wani zai zo ya zama sanadiyyar faduwar masarautar Masar din gaba daya, to banu Isra'ila sun san wannan maganar kuma suna ba wa kansu haquri da ita har Qibdawa suka dauko ta suka fadi a gaban Fir'auna din, shi kuma ya dauki matakin kashe duk wani da namiji wanda zai zama sanadiyyar rasa masarautarsa.
.
Fir'auna ya yi aiki da wayonsa gami da qarfinsa wurin ganin ya kubuta daga hukuncin Allah, sai ya yi ta kashe yara har dubbai, don dai kar a haifo wanda zai zama sanadiyyarsa, cikin qudurar mahalicci sai aka haifo shi a wani wuri ya dawo da shi hannun Fir'aunan, yadda zai raine shi, ya ciyar da shi ya tarbiyantar da shi da hannunsa a qarshe kuma ya zama sanadiyyar halakarsa da sojojinsa gaba daya (Tafsiru Ibn Kasir 3/392) in ya halaka sai jagoranci ya sake dawo wa muslunci kamar yadda yake tun farko.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)