MENENE MATSAYIN SALLAR SHAFA'I DA WUTRI?

MENENE MATSAYIN SALLAR SHAFA'I DA WUTRI?
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, malam barkanku da kokari, malam mene ne hukuncin wanda ba ya sallar Shafa'i da Wutri?

:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam, sallar Shafa'i da Wutri sunnah ce ba farillah ba, saboda haka kenan duk wanda ba ya yi ba zai sami wani zunubi ba, amma kuma wanda yake yin su ya ɗar ma wanda ba ya yi. Saboda muhimmancin Shafa'i da Wutri, har ya kasance Annabi ﷺ ba ya daina yin su a halin zaman gida  da halin tafiya, amma dai yin su ba wajibi ba ne.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)