BA SAI KIN KUNCE KAI BA YAYIN WANKAN TSARKI

*TAMBAYA* ❓

 BA SAI KIN KUNCE KAI BA YAYIN WANKAN TSARKI



malam dolene inzakai wankan tsarki saina kunce kai ko kuma inna tabbatar ruwa zai shiga ko ina basai na kunce ba nagode


 *AMSA* 👇 :

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Idan mace zata yi wankan tsarki ko kuma na ibadah kamar na juma'a ko idi, ba dole bane sai ta kunce kai ko kitson ta, amma dole ne gare ta ta tabbatar da ruwa ya jiƙa dukkan fatar kan ta, ma'ana, kamar yadda kika ce, dole ruwa ya ratsa dukkan fatar kai, insha Allahu hakan ya isar, saboda hadisin Ummu Salma daga Annabi sallallahu alaihi wa sallama

عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أَنَّ امْرَأَةً مِنَ الْمُسْلِمِينَ- وَقَالَ زُهَيْرٌ إِنَّهَا- قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنِّي امْرَأَةٌ أَشُدُّ ضَفْرَ رَأْسِي أَفَأَنْقُضُهُ لِلْجَنَابَةِ قَالَ: ((إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْفِنِي عَلَيْهِ ثَلاَثًا)). وَقَالَ زُهَيْرٌ: ((تَحْثِي عَلَيْهِ ثَلاَثَ حَثَيَاثٍ مِنْ مَاءٍ ثُمَّ تُفِيضِي عَلَى سَائِرِ جَسَدِكِ فَإِذَا أَنْتِ قَدْ طَهُرْتِ)).

Wallahu ta'aala a'lam.

Masu bukatar Shiga wannan group suyi magana ta wannan number
08132530316


https://chat.whatsapp.com/FgNSvyqReHe3rKTSuKl4zj
Post a Comment (0)