KO KUN SAN MENENE YASA JARUMI MAHESH BABU YA NUNA RASHIN SON YIN FINA FINAN BOLLYWOOD?

KO KUN SAN MENENE YASA JARUMI MAHESH BABU YA NUNA RASHIN SON YIN FINA FINAN BOLLYWOOD?


Mahesh Babu ya kasance jarumin da ya amsa sunansa jarumi ta fuskar jarumta acikin masana'antar Telugu cinema. Mutanen da dama suna ta É—aga wannan Maudu'eee sama akan ganin laifinsa bisa wannan furucin da yayi, amma koh kunsan akwai babban dalilai da suka saka jarumi Mahesh Babu yayi wannan furucin akan wannan Maudu'eee babban daLiLi anan shine John Abhram yayi wata magana marar daÉ—i wanda ya bayyana cewa bazaiyi kowane irin fina finan gefeba amatsayin supporting actor saboda yana jin kansa amatsayin babban tauraro acikin masana'antar shirya fina finai ta Bollywood. Maganar gaskiya anan itace wannan furucin yayi tasirin gaske wajen kawo damuwa tsakanin South da kuma Bollywood industry. Sakamakon wannan al'amarine, Mahesh Babu yayi magana wacce ya bayyana ra'ayinsa akan shima baya da ra'ayin yin kowane irin Film na Bollywood inda ya Qara da cewar Telugu films ana kaLLOnsi cikin kO'ina acikin faÉ—in kasarsu dama duniya baki É—aya

 "There is no need to do direct Hindi movies. Because, Telugu movies are being watched by people across the country, there is no need that I act in Hindi movies in specific 👉 abinda gwarzon jarumin ya bayyana kenan 

Toh sai azO ana ta maganar yana ji da kai ko kuma ana kwatantasa da wasu manyan jarumai na Bollywood ana kushe iyawarsa haka nan wasu suna faɗin wasu ƙana nan jarumai suna bayyana sunfi Mahesh Babu sakamakon ya fito ya bayyana ra'ayinsa wajen nuna kishin kansa da kuma cin fuskar da ake yiwa masana'antarsu sai aga laifinsa, ba wannan bane karO na farkO da jaruman BOLLYWOOD suke nuna raini koh gazawa da iyawa ta jaruman kudancin uwa Uba suna ɗaukarsu QasQantattu wanda hakan bai daceba, bana sOn Kangana Kuma banayinta amma sakamakon ta faɗi gaskiya akan wannan Maudu'eee na amshi gaskiyarta kuma na jinjina mata

Mahesh Babu jarumine da baka isa ka raina iyawarsaba kuma babu haɗin iyawa tsakaninsa da John Abraham don MAHESH BABU Superstar ne, kuma koda BOLLYWOOD industry yazo zaiyi abin agani fiye da wasu manyan jarumai da ake tunanin iyawarsu, munji mun yarda babu haɗi tsakanin BOLLYWOOD da Tollywood ta fuskar ɗaukaka, da kuma wasu ɓangarori na ƙwarewa, amma abin tambayar anan menene yasa tun ba wannan lokacinba suke yawan kwaikwayo na fina finan kudancin suke yawan Maimaita fina finansu, hakan na nuni da akwai wani sirri acikin tsarin fina finansu, akwai tasiri da Inganci na aiki da marubuta, ballantana yanzu da aka samu wani generation na wasu jarumai da suka ɗaga hankalin duniyar fina finan indiya ta fuskar ƙwarewa, wanda a kwanan nan fina finai guda biyu da suka fito RRR da KGF: Chapter 2 sun rugurguza duk wani records da akeji dasu a duniyar fina finai, kafin wannan lokacin sun fara yi musu saLLama da irinsu Baahubali, I da sauransu, menene sirri, sun duƙufa wajen samar da Labarai masu inganci da rubutu cikin inganci manazarta da kuma jarumai da suke neman kawo tseko ga BOLLYWOOD, shi kenan wannan sai yasa wasu daga cikin jaruman BOLLYWOOD su fito suna nuna kamar basu yarda da anfisuba kamar irinsu Abishekh Bachchan da John Abraham da sauransu.

Kafin wannan lokacin babu wani jarumi da yayi shura aka san suwaye kudu kuma sukayi fafutuka a Lokacin da BOLLYWOOD take da QaLubaLe da dama suke ganin kamar babu wata cinema a India bayansu suke kuma ji da kansu da raina komai na kudu, amma akwai jarumai da suka fito daga ɓangarorin wannan masana'antu na kudu sukayi fafutuka wajen sanarwar cinemas ɗinsu ƴanci, acikin wannan jarumai akwai Chiranjeevi da Yayi gwagwarmaya da jarumai da dama kuma a Lokaci Mai tsada da BOLLYWOOD take matsayin da babu wani mai iya fitowa ya nuna kansa sai ka kai ƙwararre amma haka jarumi Chiranjeevi ya fito ya fafata har yazama daga cikin zakarun da akeji dasu a waccen lokacin ya zama babu wani jarumi koh wata jaruma da zata kawo raini akansa duk da Lokacin BOLLYWOOD suna nuna ƙema ga kudanci, Kamal Hassan, Rajnikanth suma suna cikin wanda sukayi fafatawa wajen kawo sauyi da nuna suwaye south cinemas, sai gashi Yanzu ansamu jarumai da suke zuwa da Film ɗaya ya rusa manyan tarihin fina finai da Hindi take tutiya dasu, dole suji haushinsu, kada su manta wannan karon akwai irinsu Jr. NTR, PMB, Cherry, Allu Arjun da Prabhas su kaɗai sun isa su ɗagawa marasa tawakaLLi na BOLLYWOOD hankali irinsu 👉 John Abraham da Abishekh Bachchan hankali

Amma masu hankalin Bollywood kamar irinsu Big Bachchan, 3Khans, Ajay Devgn, Anil Kapoor, Hrithik Roshan, Akshay Kumar sun san gaskiya kuma sun san sirrin da yake tattare da South Cinemas don haka basa fitowa su nuna ƙiyayyarsu ko hassada akan Cinemas ɗin hasali har su kan tafi yankin suyi promoting na fina finansu su kuma je ziyarar zumunci koh wajen bukukuwa na jarumansu.

Yanzu dai muna cikin wani lokaci da idan aka shigo É“angaren fina fine akwai kimiyya da fasaha wacce take tasiri wajen manazarta da masu kaLLO don haka kada ku kasance daga cikin masu raina iyawa ko Æ™warewa sakamakon ganin sun fito daga wata industry da bata zama shahararriyaba, Tamil da Telugu basu shaharaba kamar BOLLYWOOD amma kuma suna da abubuwa da dama da suke yiwa Bollywood barazana dasu 

Don haka nima Ina goyon bayan maganar da MAHESH BABU yayi akan ra'ayinsa
Post a Comment (0)