KOWA YA GIGICE! !!!

KOWA YA GIGICE! !!!




wani mahaukaci a maiduguri ya dau wanka kawai ya shiga kasuwa. Yana shiga ya sheqa a guje yana ta fadan ihu wayyo jama'a wallahi ga su nan zuwa, sai gudu yake yana wallahi ga su nan zuwa. Haha jama'a najin haka kowa ya fara gudu. Ana neman taimako.. Kasuwa ta tarwatse kowa ya gigice can wasu gayu sun yi gudu sun gaji sai suka ga wannan mahaukacin yana ta yin haki shi ma ya gaji sai wani gaye ya matso kusa da shi yana nishi. ya ce masa wai su wane ne suka taho ne?? Sai mahaukacin ya ce wallahi YAN NEPA ne. Na gan su har da tsani sun nufo kasuwa za su yanke wuta.
Post a Comment (0)