YADDA AKE DAINA KALLON FINAFINAN BATSA (BLUE FILM)

YADDA AKE DAINA KALLON FINAFINAN BATSA (BLUE FILM)



𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamualaikum
Tambaya:
Mlm ina neman taimakone na shawara dakuma hanyoyin da zan kubutar dakaina daga kallon videos na batsa wanda hakan yajawomin nake wasa da al'aurana har sai gamsar da kaina.
Wlh mlm nayi bakin kokarina wajen naga nabari har nakan tashi cikin dare naroki Allah ya ya yafemin kuna nisancin kaina da hakan amma daga baya kuma sai nakoma ruwa kuma gashi banida halin yin aure a yanzu domin makaranta nakeyi kuma bakudin auren.
Nagode allah yasaka da alkhairi.
:
𝐀𝐌𝐒𝐀:👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Kallon finafinn batsa bashi da kyau a rayuwar mu ko kaɗan sannan ma addinin musulunci yayi mana gargaɗi game da kallon tsiraicin wani. Saboda haka, yana da kyau mu daina wannan mummunar ɗabi'ar. Amma matsalar itace duk wanda ya saba kallon irin waɗannan finafinan zai sami matuƙar wahalar dainawa. Saboda haka idan kana son daina wannan halayyar akwai hanyoyi da yawa da zaka bi.

1. Ka sa a ranka cewa babu kyau. ka goge duk fianafinan batsa dake cikin wayarka ko cumputer, wannan yanayin zai taimaka sosai wajen daina wasa da gaba, da kuma kallon finafinan.

2. Ka ƙona duk CD/tarkardun batsa. Matuƙar kana ajiye da irin waɗannan takardun ko CD na batsa, to daina kallonsu zai yi maka wahala sosai. Saboda haka, ka ƙona su sannan kuma a goge wanda yake cikin cumputer ko waya da duk wani abu daya danganci batsa.

3. Ka saka application da zai katange shafukan batsa. Ko kana amafani da waya ko cumputer duk akwai applictation da ake kira da 'anti-porn'. Shi wannan application ɗin zai hanaka shiga duk wani shafi a yanar gizo da yake da abubuwan batsa. Amma fa idan zaka saka masa lambar tsaro wato password, yana da kyau ka kira wani ya saka lambobin da baka sani ba, domin kuwa idan kaji kano son kallo babu yadda zaka buɗe ba tare da wanna lambar tsaron ba. Wasu daga cikin waɗannan application ɗin sun haɗa da: Qustodio, Microsoft family Safety, Norton Family Online, Covenant Eyes da sauransu.

4. Yanke service na yanar gizo-gizo. Idan kaji kana son kallon waɗannan finafinan a yanar gizo to abu mafi sauƙi shine ka kashe data ɗin wayarka ma gaba ɗaya ko na cumputer. Idan ma da hali ka kashe wayar ka ajiye ta.

5. Kashe lokaci da wasu abubuwan. idan ka saba zama haka kawai abu wani abinda kake yi, to lallai shaiɗan zai dinga raya maka ka kalli wannan finafinan musamman idan kai kaɗai ne a cikin ɗaki. Saboda haka ka sami abinda zai dinga kashe maka lokaci. Misali:
- ka fara motsa jiki: saboda motsa jiki yana bada wasu sinadarai a jikin mutum da suke sawa yaji daɗi.
- ka ɗan yi balaguro. Idan kana da halin barin unguwar da kake zaka iya tafiya wata unguwar na wani ɗan lokaci. Chanza waje zai taimaka sosai Chanza ɗabi’u

6. Ka gane abubuwan da suke jawo maka kallon. Zaka iya samun littafin da zaka dinga rubuta abu buwan da suka jawo maka kallon fim ɗin batsa duk lokacin daka kalla. Zama ka iya rubuta abinda ya faru a lokacin. Misali abokanai dake zancen batsa, rashin bacci, shiga instagram, gajiya da sauransu.

7. Ka nemi aikin yi. Bincike ya nuna cewa idan mutum bashi da aikin yi suna iya fadawa cikin nema abubuwan kala-kala a cikin yanar gizo. Daya daga ciki shine fara kallon hotuna/finafinan batsa. Saboda haka ka nemi aikin yi da zai kashe maka lokaci. Zaku yarda dani idan nace mutumin dayake son aikinsa zai dinga yin aikin ne har a lokacin dana hutu ne, kenan bazai ma dinga tinanin kallace-kallacen batsa ba.

8. Ka nemi hanyar katange abubuwan dake jawo maka. Idan da hali ka katange abubuwan dake jawo maka kallon duk gaba ɗaya, amma idan bazai yiwu ba, sai ka fara kaɗan-kaɗan. Misali, idan kallon talla ne a TV yake taso maka da sha'awar kallon, sainka guji kallon TV a lokacin dakasan za'a saka irin waɗannan tallukan. Idan kuma babu yadda za'ayi ka guje wa abubuwan dake taso maka da sha'awar, to sai ka guje su a kwakwalwarka. Misali sai ka dinga hango kanka cewa gasu sunzo maka kuma gashi ka guje musu ta hanyar tinanin wani abun kamar abinci, tattaki da sauransu.
Post a Comment (0)