DUK MINTI BIYU SAI NA YI TUSA, YAYA SALLATA ??
Tambaya
Salamun'alaikum, Malam Wai akwai sallah ga wanda in yana sallah sai ya fitar da iskar tusa kuma duk sallah yake hakan koda ace yayi kashi kafin yayi sallahr ,amma in har ya zo sallah sai ta futo koda ace zayyi alwala sama da 10,
Amsa
Wa alaikum assalam, akwai sallah akan shi, ba za ta taba faduwa ba akansa, ya wajaba a gare shi ya yi alwala yayin kowacce sallah, dağa nan duk abin da ya fito yana sallah ba zai cutar da shi ba, tun da in aka ce ya sake alwala yayin fitowar kowacce tusa ba zai iya ba, zai kuma shiga cikin wahala, Sharia ba ta dorawa rai sai abin da za ta iya, kamar yadda ayoyi da hadisai da yawa suka tabbatar da haka.
Babu takurawa da kunci a cikin Addinin musulunci kamar yadda ayar karshe a suratul Hajji ta tabbatar da hakan.
Don neman Karin bayani duba : Alfawakihuddawany na Annafraawy 1\340.
Amma idan tusar ba'a mafi yawan lokuta take fitowa ba ya wajaba ya sake alwala duk sanda ta fito, saboda sallah ba ta ingantuwa saida alwala.
Kula da wasuwasin abu ne mai muhimmancin gaske, saboda da yawa Shaidan ne yake busa a duburar dan'adam amma ba tusa ba ce, wanda ya ji haka, to kar ya fita daga sallarsa, har sai ya ji iska ko kara ta fita, kamar yada hadisin Bukhari ya tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
24\04/2016