DUNIYA KURKUKUN MUMINI
Manzon Allah (SAW) ya ce; "Ita duniya kurkukun muminine, kuma aljannar kafirice"
صحيح الترمذي 2324
An ruwaito cewa lokacin da Hafiz ibnu Hajar yake alkalin alkalai ya zo wucewa ta kasuwa acikin shiga mai kyau da kaya na alfarma, sai ya hadu da wani bayahude yana sayar da mayi, kayansa duk sun chakude da mayin, yana cikin datti da wahala, sai wannan bayahuden ya tare shi ya rike linzamin dokinsa yace masa, ya kai malamin musulunci kana raya cewa Annabinku yace "Duniya kurkukun mumini ne, aljannar kafirice" to kai awana kurkukun kake, ni kuma gayamin wace aljannar nake ciki?? Sai ibnu Hajar yace masa, bisa La'akari da abunda ya tanadamin alahira na jindadi to ayanzu kamar ina kurkukune, haka kuma kaima, la'akari da irin abunda aka tanadama na azaba to ayanzu kamar kana aljannah ne, dagajin wannan bayani sai wannan bayahude ya musulunta".
فيض القدير 3/546
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah