JANABAR GWAURAYE A LOKACIN SANYI
*Tambaya*
السلام عليكم ورØمه الله
Fatan alkhairi.
Dama karin bayani ne nake so game da janaba, idan ta samu mutum a lokacin sanyi?
Jazakallahu khairan.
*Amsa*
Wa alaikum assalam
In har ya zama in ya yi wanka zai cutu, yana iya yin taimama saboda hadisin Amru Dan Ass lokacin da ya yi janaba ana tsananin SANYI, sai ya ki yin wanka, saboda tsoran lalura, ya taba kasa, ya shafawa fuskarsa da hannayansa zuwa ku'u, ya je ya yi sallah.
Da aka gayawa Annabi SAW sai ya yi murmushi, hadisin sai yake nuna halaccin taimama ga Gwauron da bai samu ruwan zafi ba lokacin SANYI.
Allah ne mafi Sani.
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18-01-2023
Miftahul ilmi
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM ⇨https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248