TA YI AURE DA CIKIN SHEGE

TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE  


Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.

Yanzu sun yi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

AMSA :
Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.                              
 Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.                     
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud : 1847. Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79
 A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba ÅŸu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.
Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
27\2\2016
Post a Comment (0)