*_BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI GIYA A HARANCI_*
*Tambaya*
Assalamu Alakum.
Malam ina da tambaya kamar haka,shin tabar wiwi tana daukan dukkanin hukunce hukuncen da suka hau kan giya (barasa)ko kuwa akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya a Zauren Fiqhu.nagode.
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, mutukar ta amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za dauki dukkan hukunce-hukuncen giya na haramci.
Annabi S.A.W yana cewa "Dukkan abin da yake sanya Maye giya NE, kuma dukkan giya haramun ce" kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi ingantacce, wannan sai ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.
Allah ne mafi Sani.
05/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.