*_MIJINA YA SADU DA NI, KAFIN NA YI WANKAN HAILA?_*
*Tambaya?*
Assalamu alaykum, malam inada tambaya, malam mi ar hukuncin mace taqare haila batayi wanka ba mijin ta ya sadu da ita?
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne: ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka fahimta a aya ta 222 a suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da yankewar jinin haila kawai.
Riko da mazhabar farko shi ne ya fi saboda Allah ya kira haila da cuta.
Babu wata kaffara ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan yankewar jinin haila.
Allah ne mafi sani:
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.*_MENENE TA'ARFIN QUR'ANI DA HADITH_*
*👈 القرآن لغة:* مصدر قرأ بمعني قرأ وهو الجمع والضم.
*👈 القرآن اصطلاحا :* هو كلام الله المنزل علي نبيه محمد (صلى الله عليه وسلم)المعجز بلفظه،المتعبد بتلاوته المنقول إلينا بالتواتر ،المكتوب بين دفتي المصحف، من أول سورة الفاتحة الي آخر سورة الناس.
*👈 الحديث النبوي* أو السنة النبوية عند أهل السنة والجماعة هو ما ورد عن النبي محمد صلى الله عليه وسلم من قول أو فعل أو تقرير أو صفة خـَلقية أو صفة خُلقية أو سيرة سواء قبل البعثة (اَي بدء الوحي والنبوة ) او بعده.
*MA'ANA: 👇👇👇*
*👉Al Qurani :* shine zancen Ubangiji wanda ya sauka ga Annabi Muhammad (SAW), mai mu'ujizar fada, tilawarsa ibadace, wanda jama'a masu yawa na daga sahabbai da tabi'ai suka ruwaito shi Izuwa garemu, rubutacce a mushaf, daga farkon suratul Fatiha izuwa karshen suratun Naas.
*👉 Hadisi:* shine abinda ya samu daga Annabi (SAW) na daga magana, ko aiki, ko wani yayi abin a gabansa bai hanaba sai ma karfafa abin yayi, ko siffa ta halayya, ko siffa ta halitta , ko wani labari daga gareshi, sawa'un alokacin da Aka saukar masa da Annabta ko bayan lokacin.
✍ Rubutawa:- *Malama Ummu Hamdan wa Hameed*
Gabatarwa:- *Dalibin malama*