WASAN KANIN MIJI A MUSULUNCI
Wasan Kanin Miji dai shi ne Irin Wasan da ake yi tsakanin Matar WA da kuma kanin Mijin ta. A Musulunce, Wasan Kanin Miji Haramun ne. Domin an karbo daga Dan Aamir Radiyallahu Anhu cewa : Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace ; "ku guji shiga wajen mata", sai wani Mutumin Ansar ya ce, "Ya Manzon Allah! Yaya kake ganin shigar kanin Miji? Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace ;" Kanin Miji ai MUTUWA ce (wato shi ne mafi Sharri) ". Duba cikin littafin Sahih Al Bukhari Hadisi na dubu biyar da dari biyu da Talatin da biyu.
To anan, idan muka dubi wannan Hadisi da kyau, za mu Fahimci cewa, Kanin Miji shi ne mafi Sharrin duk wani mutum da zai kusanci matar aure ko kuma wacce ba Muharramar sa ba domin Shaidan na iya amfani da shi ta hanyoyi da dama wajen Wargaza aure.
To amma bari mu Waiwayi Mallam Bahaushe muji shi kuma me yace dangane da Kanin Miji. Hausawa, Musamman ma dai mata, sukan yi wata Bahaguwar Karin Magana in da suke cewa : "Ba Haka rai Ya So ba, Kanin Miji Ya Fi Miji Kyau!" To in muka lura da Wancan Hadisi da muka Ambata da kuma wannan Karin Magana, zamu ga cewa a kwai matsala Babba.
A Takaice, ga kadan daga cikin Illolin da Wasan Kanin Miji ke Haifarwa ;
* Zubewar Mutunci.
* Kawo Zargi a Tsakanin Ma'aurata.
* Baiwa Shaitan damar da zai Wargaza aure, dama haka yake so.
* Zina.
* Mutuwar Aure.
* Lalacewar Zumunci.
* Wanzar da gaba a Tsakanin Ma'auratan da kuma 'Yan Uwa.
Wadannan da kuma wasu Makamantan su, su ne Matsalolin da Wasan Kanin Miji ka iya Haifarwa.
Ina Fatar Allah Ya Tserar da mu daga Sharrin Shaidan.
Ya Allah Ka Azurta Mu Da Kyakkyawar Fahimta Ameen.
©
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees Haimanraees@gmail.com
08185819176
January 2017