SHIN MUTUM ZAI IYA YIWA IYAYEN SA WA'AZI?

*_SHIN MUTUM ZAI IYAYIWA IYAYENSA WA'AZI?_*


                               *Tambaya*
Wai shin mutum xai iyayiwa iyayensa wa'axi, Ko kuma inyaga baxai iyaba sai yasamu wanda suke fadamasa yaji suka mar nasiha akan abinda yakeyi, Bayan hakan yafaru sai mahaifinnasa yace wlh shi baiyafemasa ba sannan yace inhar shine mahaifinsa baxai daba jindadi ba arayuwarsa , to waishin yahukuncin yake a addini

                                     *Amsa*
Assalamu Alaikum, Babu shakka ana yiwa kowa wa'azi har mahaifa, sai dai da bambamci yadda akewa mahaifa wa'azi da kowa.

                                   *Hujja*
Annabi Ibrahin A.S ya yiwa mahaifinsa wa'azi amma cikin laluma ta tausasa harshe, yana kiransa da *YA ABATI* (ya baba) kamar yadda suratul (MARYAM) taba da labari.


                                  *Nasiha*
Duk wanda zai yiwa iyayensa wa'azi to ya kasance mai biyayya ne a tare da su, ya kasance mai yi musu hidima, da duk sauran mu'amala mai kyau wacce ta rubanya yadda akewa kowa wanda basu ba.
Kuma babu laifi idan da ya saka wani wanda iyaye suke ganin girmansa ya yi musu wa'azi.

                                 *Hukunci*
Wanda duk ya kasance haka to babu laifi ko da iyaye sunyi masa baki, insha Allah babu abin da zai sameshi sai dai yayi kokari kada ya gajiya dayi musu wa'azi ta duk hanyar da zai sa su iya fahimta.

*ALLAH S.W.A YA KARA FAHIMTAR DA MU AMEEN*

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)