IYALAN MU DA SALLAH 01

*🎊IYALAN MU DA SALLAH 01🎊*

🎉Kamar yanda muka sani ne muna cikin kwanaki goma mai albarka, kuma suna gabda wucewa. Sai kuma shirye-shiryen bikin babban sallah, kamar yanda muka saba duk shekara.

🎉Ina so iyaye su kula da wadannan abubuwan yayin da bikin sallah ya fara. Musamman uwa domin 95% na tarbiyya a hannun ki yake.

🎉Ku yi kokarin yi wa 'ya'yanku kayan sallah, da kuma kokarin siya musu dukkan abun da za su bukata musamman ga mace. Kuskure ne babba a ce saurayin 'yarki shi zai mata kayan sallah, dama dukkanin abin da ya shafe ta. In dai ba yaro ya zo an sa rana ba, to a guji kar'ban abin hannun sa, saboda yawancin maza suna yiwa yan mata kyauta ne da wata manufa. An san namiji ya kan yiwa mace kayan sallah amma sai in an sa musu rana, kuma duk da haka ba shi yake nuna ba zaku mata ba saboda shi zai mata. Kun ga daga lokacin da kuka kasa sauke nauyin ku na iyaye sai yaron ku ya fara waige-waigen ina ne zai samu. Saboda ta ga dukkan kawayen ta suna da shi ita kuma ko oho.

🎉Idan kuma ba za'a samu yi musu ba to ku dage wurin yi musu nasiha akan su yi hakuri da abin da suka samu. Da fada musu in da akwai da an musu, musamman wannan lokacin da abubuwa suka yi zafi. In babu a ba su hakuri kuma a fahimtar da su.

🎉Kuskure ne babba ka ji uwa tana cewa 'yarta ba zamu sami daman yi miki kayan sallah ba, sai dai in zaki fada wa saurayi ki (roke shi) akan ya dinka miki. Kun ga wannan ba karamin zubar da mutuncin 'ya yake ba. Kuma idan ya gane cewa ku kwadayayyu ne haka zai rinka mata kyauta don kawai ya kwanta da ita. Kun ga kun jefa 'yarku ga halaka, in ma bai kwanta da ita ba ya aureta to kun siyar da mutuncin ku. Don wani saurayin har qannin yarinyar saurayin ne yake yi musu.

🎉Sannan kula da irin shigan da 'ya'yanki maza da mata za su yi. Yana da mutukar ban haushi a ce baka iya banbance 'yar musulma ko dan musulmi da sallah, saboda shiga da aka yi mai muni. Uwa ke ya kamata a ce kin sa ido wurin irin 'dinkunan da suke yi, idan wanda bai yi dai-dai da addinin musulunci bane ki hana ta sanyawa. Zaka ga wata duk abun da yarinya ta sa za su barta sai ace ai sallah ne. Shi yasa yawancin matsalar da mata suke samu daga shigan da suka yi ne. Domin shine zai saka namiji ya ji sha'awar 'yarki, don shi mara tarbiyya wacce ya ke fara kalla ita ce wacce tayi shigar banza, sai ya dauka 'yar iska ce, ko da kuwa ba haka take ba. Don haka su yi shigar su ta kamala, su lullube kwalliyar da zai fito musu da siffofin jikin su.

*🖎Sadeeya Lawal Abubakar*

*📚MARKAZUS SUNNAH.*

*📞Zaku iya shiga group din ta wainnan numbers din 08034643244 08089074217*

Post a Comment (0)